'Dan Nigeria Mai Tallan Mangwaro Ya Samu Gurabe 6 Don Zuwa Ƙasar Waje Yin Digirin Digirgir Kyauta

'Dan Nigeria Mai Tallan Mangwaro Ya Samu Gurabe 6 Don Zuwa Ƙasar Waje Yin Digirin Digirgir Kyauta

  • Onyeka Chukwudozie matashi ne da jami’o’i 6 dake Australia da California suka yi tayin daukar nauyin karatun sa na digirin-digirgir
  • Matashin wanda ya bayyana wannan daukakar a shafin sa na Linkedln ya bayar da labarin yadda ya yi tallar mangwaro da lemu a baya
  • A cewar sa, ya samu wadannan tayin ne bayan jami’o’i da dama sun ki amincewa da karatun sa a shekarun da suka gabata

Wani dan Najeriya, Onyeka Chukwudozie ya samu tayin karatun digirin-digirgir daga jami’o’i 6 daban-daban dake Australia da California, The Punch ta ruwaito.

Matashin ya bayyana wannan nasarar ne ta shafin sa ba Linkedln inda ya ce har tallar magwaro da lemu ya yi a kasuwanni a baya.

Dan Nigeria Mai Tallan Mangwaro Ya Samu Gurabe 6 Don Zuwa Kasar Waje Yin Digirin Digir-Gir Kyauta
Dan Nigeria Mai Tallan Mangwaro Ya Samu Gurabe 6 Don Zuwa Kasar Waje Yin Digirin Digir-Gir Kyauta
Asali: Facebook

A cewar sa, ya samu wannan damar cigaba da karatun ne bayan jami’o’i da dama sun hana shi cigaba da karatu a shekarun baya.

Chukwudozie ya kammala digirinsa na farko a jami’ar Legas a shekarar 2016 kuma ya kammala da digiri mai daraja ta farko.

Duk da damar da ya samu, ya zabi ya karanta fannin Biological Sciences a jami’ar California da ke San Diego.

A cewar Chukwudozie;

“Yanzu kam mafalki na ya zama gaske. Zan fara karatun digirin-digirgir a fannin Biological Sciences a daya daga cikin manyan jami’o’in duniya ta UC San Diego (Jami’ar California dake San Diego). A baya har tallar mangwaro da lemu na yi a kasuwanni da tituna duk don in tallafa wa iyaye na.
“Yanzu sai ga ni na samu tayin ci gaba da karatun digirin-digirgir daga jami’o’i da dama kamar jami’ar California San Diego, jami’ar Rice, sannan na samu tayi biyu daga jami’ar Purdue, jami’ar Kansas da kuma jami’ar Melbourne duk a Australia. Wannan ya biyo bayan kin amincewa da ni da jami’o’i da dama suka yi wanda ya matukar sosa min rai na."

A cewar sa, “A gaskiya shekaru 3 da nayi jami’o’i suna hana ni damar ci gaba da karatu na fuskanci radadi, wahala, hakuri da kuma juriya. Bayan na kammala digiri na a jami’ar Legas ina ta fatan ganin na cigaba da karatu.
“Sun yi ta dakatar dani duk da yadda na dade ina rubuce-rubuce da bincike iri-iri. Yawancin kin amincewar da na fuskanta daga jami’o’i masu matsakaicin daraja ne amma hakanan na jajirce. Daga nan ne na fara neman makarantu masu daraja kuma ga shi yanzu na samu.”

Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

A wani labarin daban, wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.

An aurar da matar biyu ne bayan mahaifinsu, Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.

Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel