Babban zunubi ne talaka ya dube ni ya ce yana kauna ta, Jarumar Fim
- Wata jarumar finafinan Nollywood, Onyii Alex ta bayyana irin jerin mazajen da za su iya gabatar da kawunan su gare ta da sunan soyayya
- Jarumar ta ce zunubi ne ga talakan namiji ya kalle ta da idon soyayya kuma wajibi ne mutum ya kasance mai wadata matsawar yana son ta saurare shi
- Ta ce talaka zai iya hango ta daga nesa ta dinga burge shi amma babu dalilin da zai sa taho tsummai-tsummai gare ta don ba zai taba kayatar da ita ba
Jarumar Nollywood, Onyii Alex ta bayyana yanayin jerin mazajen da suka dace su mika kokon barar su da sunan soyayya da ita.
Kamar yadda The Nation Online ta ruwaito, ta ce wajibi ne namiji ya kasance mai kwazo gaske da kuma dukiya mai tarin yawa.

Kara karanta wannan
Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba

Asali: UGC
A cewar Alex, zunubi ne ga talaka ya dube ta ya furta mata soyayya musamman yadda ta dage tana neman na kan ta kuma ta na da rufin asiri, The Nation Online.
A cewar jarumar, za ta iya burge talaka daga nesa amma babu dalilin da zai sa ya matso gare ta matsawar bai tara kudade ba don ba za ta taba iya amfani da dukiyar ta don tallafa masa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zunubi ne talaka ya kalle ni ya ce yana so na... Ta ina? Ka dage kawai ka nemi kudi don ba a yi ni don wahala ba.
Babu damuwa in har daga nesa zan burge talaka!!! Buri na shine dukanmu mu nema kuma mu tara dukiya ba wai daya ya dinga warwara daga daya ba,” a cewar Onyii.
Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan
A wani labari na daban, shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Muhammed Babandede, a ranar Juma'a ya yi bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan NIS na kokarin tsare iyakokin kasar nan.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron sirri da yayi da shuagaban kasa, Babandede ya ce NIS ta kirkiro da sabbin tsare-tsare domin duba yanayin shige da fice bakin haure a kasar nan ba bisa ka'ida ba.
Kamar yadda yace, hukumar ta samu kayan aiki masu kyau domin taimaka wa wurin fallasa jama'ar da ke zama a kasar nan ba bisa ka'ida ba bayan hatimin shigowa kasar nan nasu ya gama aiki.
Asali: Legit.ng