A fara shirin yaki a zabe mai zuwa, 2023 dabam ce – Kwankwaso ya yi wa ‘Yan PDP huduba

A fara shirin yaki a zabe mai zuwa, 2023 dabam ce – Kwankwaso ya yi wa ‘Yan PDP huduba

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP na Kano
  • Tsohon Gwamnan na jihar Kano ya fada wa mabiyasa su fara shirin 2023
  • Kwankwaso yace akwai bukatar ‘Ya PDP su hada-kai, su yi waje da APC

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga mabiyansa da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP su shirya yakin zaben 2023.

Daily Trust ta ce Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne jagoran Kwankwasiyya ya bayyana haka a lokacin da yake gana wa da ‘ya ‘yan PDP na Kano.

Tun daga ranar Juma’a, 27 ga watan Agusta, 2021, Rabiu Musa Kwankwaso ya fara yin zama da ‘yan jam’iyyar PDP bayan ya dawo daga garin Abuja.

Kowace mazaba ta tura shugaban jam’iyya, jagororin Kwankwasiyya da shugabannin mata da ‘yan Kwankwasiyya Scholars a wajen taron da ake yi.

Kara karanta wannan

Yadda aka je har gida, aka maƙure babban ‘Dan Sanata Na Allah inji Gwamnatin Kaduna

Shugaban cibiyar yada labarai ta Kwankwaso Media Centre, Sanusi Bature ya fitar da jawabi, ya ce Kwankwaso ya yi kira ga mabiyansa su hada-kansu.

Kwankwaso wanda ya wakilci Kano ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019 ya zargi gwamnatin Ganduje da kashe harkar ilmi da kiwon lafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a taron PDP Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Muna da makiya a matsayinmu na ‘ya ‘yan hamayya, mu dunkule kamar tsintsiya, mu yaki makiyanmu da suka rusa harkar ilmi da kiwon lafiya."
“Ina so ku shirya wa yaki mai zuwa, 2023 za ta zama dabam, yadda ta sha ban-bam ta sa akwai muhimmanci mu hada kai, mu yaki makiyan Kano.”

Hadimin tsohon gwamnan, Saifullahi Hasan yace Sanata Kwankwaso ya zauna da shugabannin PDP na Kibiya, Rano, Bunkure da Rogo a yau da rana.

A jiya ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta, 2021, Kwankwaso ya yi wa iyalin tsohon shugaban dattawan PDP na Kano, Aminu Baba Danbaffa ta’aziyya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Siyasar 2023

Yayin da yake jinya a kasar waje, Sarakunan jihar Legas sun yi wa tsohon gwamna Asiwaju Bola Tinubu mubaya’a a wani taro da aka gudanar kwanaki.

Da aka tambayi Obas ko za su yi Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023, duk sun nuna goyon bayansu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng