Sarakunan jihar Legas sun bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu a takarar Shugaban kasa

Sarakunan jihar Legas sun bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu a takarar Shugaban kasa

  • Sarakunan Legas za su goyi bayan Bola Tinubu idan zai yi takara a 2023
  • Kawo yanzu jigon na APC bai fada wa kowa ya na neman shugabanci ba
  • Da aka yi wani taro, an samu goyon-bayan duka Sarakunan kasar Legas

Lagos - Masu rike da sarautar gargajiya a kasar Legas sun yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mubaya’a a zaben shugaban kasa mai zuwa da za ayi.

Jaridar PM News ta ce Sarakunan sun nuna goyon bayansu Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa.

Sarakunan sun bayyana goyon bayansu a karkashin jagorancin Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, a wani taro da aka shirya a Eko Hotels a Victoria Island.

A wannan taro da aka yi a Eko Hotel & Suites, an tattauna a kan matsayin masu sarautar gargajiya wajen kawo zaman lafiya da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka rabawa mabukata kayan garan matar Yusuf Buhari, Zahra Bayero

Rahoton yace sarakunan sun nuna suna tare da jigon jam’iyyar APC mai mulki, za su mara masa baya ya zama shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari.

Sarakunan sun bayyana ra’ayinsu a wani sashen taron da Osolon kasar Isolo, Oba Kabiru Agbabiaka, ya jagoranta, wanda shi ne sakataren majalisar sarakunan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarakunan jihar Legas
Sarakuna suna tare da Bola Tinubu Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Oba Kabiru Agbabiaka ya tambayi Sarakunan ko suna goyon bayan Tinubu ya zama shugaban kasa.

PM News ta ce duka Sarakunan da suka halarci wannan zama sun nuna goyon bayansu ta hanyar karkada gashin bindin dokin da ke jikin sandar girmansu.

A duk lokacin da tsohon gwamnan na jihar Legas ya fito ya shaida wa Duniya cewa zai nemi kujerar shugaban kasa, Sarakunan za su bada goyon-bayansu.

Sai da zaman lafiya ake cigaba

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi, Dr. Wale Ahmed, ya yi kira ga Sarakuna su dage wajen raba rigingimu a kasarsu domin kawo zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan shekara da shekaru, Kwankwaso da Ganduje sun hadu

“Matsayinku ya zarce rike masarautun gargajiya da tsare al’adu a jiha irin wannan ta mu, inda zaman lafiya yake taimaka wa wajen kawo wa jihar cigaba.”

PDP ta fara lissafin 2023

A yau aka ji jam’iyyar PDP ta na iya damka wa ‘Dan Arewa tikitin tsaya wa takarar Shugaban kasa a 2023, sannan a ba 'dan kudu kujerar shugaban jam'iyya na kasa.

Kusoshin Jam’iyyar PDP sun fara lissafin yadda za a tunkari zaben Shugaban kasar. Atiku, Obasanjo da Tambuwal suna kokarin ganin na-su sun rike jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel