An gurfanar da Fasto mai shekaru 70 a gaban kotu kan damfarar N870,000 na siyan 'man sihiri'

An gurfanar da Fasto mai shekaru 70 a gaban kotu kan damfarar N870,000 na siyan 'man sihiri'

  • An maka wani fasto mai shekaru 70 a kotu bayan ya lamushe N870,000 da sunan zai samar da man sihirin da ake amfani da shi wurin wanke daloli
  • Fasto Emmanuel Bello, mazaunin Idimu, ya bayyana a gaban kotu bisa zargin da ake masa na ha’inci har da amsar kudade da kuma sata
  • Ya amshi kudin ne daga hannun Bilkisu Ilabisi kuma ya kasa samar da man sihiri, kuma an yi kokarin amsar kudaden daga hannunsa amma ya murje ido ya ki bayarwa

Jihar Lagos - An maka wani fasto mai shekaru 70 a kotu bayan ya amshe N870,000 da sunan zai sayo 'man sihiri' wanda ake amfani da shi wurin gyara daloli da wanke su.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Emmanuel Bello, mazaunin Idimu, ya bayyana a gaban kotun majistare da ke Ikeja a jihar Legas don ana tuhumar shi da laifin ha’inci na amsar kudade da yaudara har da sata.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar kwastam sun cafke wata mota dauke da bindiga da harsasai

An gurfanar da Fasto a gaban kotu kan damfarar N870,000 na siyan 'man sihiri'
An gurfanar da Fasto a gaban kotu kan damfarar N870,000 na siyan 'man sihiri'. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

An gabatar wa da kotun yadda Bello ya warwari kudade daga hannun Bilkisu Olabisi bayan ya yi mata alkawarin samo mata man sihiri wanda ake amfani dashi wurin wanke daloli da tsaftace su.

Wanda ake zargin tare da wasu sun aikata laifin a ranar 2 ga watan Maris a wuraren Idimu da ke jihar Legas, kamar yadda sifeta Mojkrade Edeme ya sanar da kotu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ya amshi kudaden daga hannun ta, ta yi iyakar kokarin ganin ta karbi kudin daga hannunsa amma hakan ya ci tura. Shiyasa ta kai kararsa don a damke mata shi, a cewar dansandan.

Laifin da ya tafka ya ci karo da sashi na 287, 314 da 411 na dokar laifukan jihar Legas na 2015, Daily Trust ta ruwaito.

Bangare na 287 sun sanya hukuncin ya zama shekaru 3 a gidan gyaran hali, sannan bangare na 314 ta yanke shekaru 15 sakamakon amsar kudade bisa karya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Alkalin kotun O.O Raji, ya bayar da belin mai laifi ya zama N100,000 da kuma tsayayye guda daya

Raji ya ce wajibi ne tsayayyen ya kasance mai aiki mai kyau, sannan ya gabatar da shaidar biyan kudin haraji na shekaru biyu ga gwamnatin jihar Legas.

Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce jami’an ta sun kwace bindigogi kirar AK-47 guda 25 da sauran miyagun makamai guda 6,460 cikin watanni 6 da suka gabata.

Punch ta ruwaito cewa, ya kara da bayyana yadda suka kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne guda 352 wadanda suke da masaniya da laifuka 221 daban-daban cikin wannan lokaci.

Jami’in hulda da jama’a, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya bai wa manema labarai a ranar Juma’a, inda yace tun daga watan Maris suke kamen har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Bayan da Taliban ta karbe mulkin Afghanistan, Amurka ta kai hari da jirgi

Asali: Legit.ng

Online view pixel