Ronaldo ya yi wa Magoya-bayan Juventus maganar karshe, ya koma wasa a Old Trafford

Ronaldo ya yi wa Magoya-bayan Juventus maganar karshe, ya koma wasa a Old Trafford

  • Cristiano Ronaldo ya yi bankwana da Magoya-bayan Juventus da kasar Italiya
  • ‘Dan wasan ya rubuta jawabin sallama bayan an bada sanarwar ya canza kulob
  • Tauraron ya ji dadin irin girmama shin da aka yi a Turin, ya ce ba zai manta ba

England - Cristiano Ronaldo ya aika wani sakon bankwana na musamman ga magoya bayan kungiyar Juventus, yayin da ya koma Manchester United.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘dan wasa Cristiano Ronaldo ya aika wannan sako ne a shafinsa na Instagram, ya na mai gode wa duk magoya bayan Juventus.

Da yake sallama a dazu, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa ya bada duk karfinsa ga kungiyar Italiyan a lokacin da yake dauke da rigar su na shekaru uku.

A bankwanan da ya yi a ranar 27 ga watan Agusta, 2021, Ronaldo yace ba zai taba manta wa da Juventus ba domin kungiyar ta bar tambari a cikin zuciyarsa.

Kara karanta wannan

Ronaldo ya bukaci ya bar Juventus, ya na tangaririn neman wanda zai iya biyan albashinsa

“A yau na bar wannan kulob mai ban-kaye, kungiyar da ta fi kowace a kasar Italiya, daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke kaf Turai.”

Ronaldo
Cristiano Ronaldo a Juventus
Asali: Getty Images

“Na bada zuciyata da rai na a lokacin da na ke Juventus, kuma har na tashi, ina kaunar birnin Turai."

Goal.com ta rahoto CR7 yana cewa “tiffosi bianconeri” sun girmama shi, ya yi kokarin saka wa ta maida hankali a kowane wasa, a kowace kaka, a kowane gasa.

“Zan cigaba da zama daga cikinku. Yanzu kun shiga tarihi na; ina ji cewa na shiga cikin na ku. Italiya, Juventus, tiffosi bianconeri, Turin, za ku kasance a zuciyata."

Ya zaman Ronaldo a Seria A?

‘Dan kwallon na Portugal mai shekara 36 a Duniya ya ji dadin soyayyar da aka nuna masa a Turin, inda ya lashe gasar Seria A sau biyu da Copa Italiya a 2020.

Kara karanta wannan

PSG Ta Yi Watsi da Makudan Kudin da Real Madrid Ta Saka Wa Mbappe, Harry Kane Ya Bayyana Makomarsa

Duk da Ronaldo ya ci kwallaye 101 a wasanni 134, ‘dan wasan bai iya taimaka wa Juventus wajen samun nasara a gasar kofin Turai a shekaru ukun da ya yi ba.

Tsohon ‘dan wasan na Real Madrid ya dawo wasa a kasar Ingila, inda ya yi fice. Manchester United ta bada sanarwar dawowan Ronaldo bayan shekaru 12.

Real Madrid na neman Mbappe

A makon da ya gabata ne kuka ji cewa kungiyar Real Madrid ta mika Naira Biliyan 80 a kudin Najeriya domin ta dauke Kylian Mbappe daga PSG a kakar bana.

Real Madrid tana neman a saida mata ‘dan kwallon a kan fam miliyan $188. PSG ta ki karbar wannan kudi, don haka Real ta kara tayin farko da ta yi a jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel