Bidiyon ango da yayi wa amarya liƙin maƙuɗen kudi, ya kwashe kayansa bayan liyafa

Bidiyon ango da yayi wa amarya liƙin maƙuɗen kudi, ya kwashe kayansa bayan liyafa

  • Bidiyon wani ango gajere mai kiba ya bayyana inda yake yi wa amaryarsa ruwan kudi a wurin liyafa ya bayyana
  • Sai dai abun mamakin shi ne yadda amaryar mai sanye da kayan kabilar Kanuri bata ko taka rawa ba
  • Daga bisani an ga sabon bidiyo inda abokan ango ke taya shi gyara kudin kuma yana waya kan yadda zai mayarwa masu kudin kayansu

Liyafar biki - Wani bidiyo ya bayyana wanda aka ga wani mutum yana ta watsa wa amarya kudade masu yawan gaske yayin da amaryar ta ke tsaye kamar bishiya ko murmushi bata yi ballantana rausayawa yayin da yake ta mata ambaliyar kudade masu yawan gaske.

An ga wani bidiyon na daban wanda aka ga wannan dai mutumin mai watsa kudade sanye da sutturarsa tare da wasu maza biyu daban suna tattara kudaden da ya manna a wurin bikin.

Kara karanta wannan

Rufe Makarantun Kaduna: Iyayen Ɗalibai Sun Ce Sun Fara Tura Ƴaƴansu Koyon Ɗinki Da Walda

‘Yan Najeriya da dama sun yi ta cece-kuce a kan aukuwar wannan lamari mai ban mamaki a wannan biki.

Bidiyon ango da yayi wa amarya likin makuden kudi, ya kwashe kayansa bayan liyafa
Bidiyon ango da yayi wa amarya likin makuden kudi, ya kwashe kayansa bayan liyafa. Hoto daga @saintavenue_ent1
Asali: Instagram

Duk da dai ba sabon abu bane a ga baki a biki suna watsa kudade

A wani bidiyo wanda Saintavenue_ent1 suka wallafa a Instagram, an ga wata amarya tsaye kamar ice sanye da wasu sutturu irin na Kanuri, ba ta murmushi ko kadan yayin da angon ta yake lika mata kudade.

Sai dai abin mamakin shine yadda ko damuwa amaryar ba ta yi ba da shi yayin da ya cigaba da mata ambaliyar kudaden.

Ango ya kwashe kudinsa tsaf

An ga wani bidiyo na daban na wannan mutumin da ya gama ruwan kudin ga amaryar nan zaune a daki tare da wasu maza guda biyu sanye da wannan sutturar da ya sa wurin bikin suna tattara kudaden da ya gama mannawa a bikin.

Kara karanta wannan

Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

An ganshi yana yin waya sauran mazan suna tattara kudaden baje-baje a tsakar dakin.

A wayar an ji yana cewa in har wasu daga cikin kudin suka bata, sai an tuhumi DJ, wato mai kayan kida.

Wannan maganar tashi kuwa ta sa jama'a suka fassara cewa aro kudaden yayi kuma ana gyara su ne domin a mayarwa da masu kudin kayansu.

Obasanjo: Masu son ganin rabewar kasar nan makiyanta ne, za su ji kunya

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Juma’a ya ce yawancin makiyan Najeriya wadanda suke fatan rabewar ta ba za su ci nasara ba, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takarda wacce hadiminsa na harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya saki, ya ce Obasanjo ya ce kasancewar ‘yan Najeriya tare ya fi sauki a kan rabewarsu.

An ruwaito yadda yayi wannan jawabin yayin kaddamar da wani littafi mai suna “My Life and Times”, wanda Sunday Mbang ya rubuta.

Kara karanta wannan

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel