Da duminsa: An alanta neman tsohon sojan da yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram

Da duminsa: An alanta neman tsohon sojan da yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram

  • Gwamnati ta sammaci tsohon jami'in leken asiri da ya ce akwai gwamnoni da Sanatoci cikin masu daukar nauyin Boko Haram
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ana shirin kwace Fasfot dinsa zuwa kasar waje
  • Tsohon Soja yayi fashin baki ne lamarin tsaro da harin da aka kai NDA

Abuja - Gwamnatin tarayya ta alanta neman tsohon Sojan ruwa, Commodore Kunle Olawunmi, ruwa a jallo kan hirar da yayi kan shirin 'Sunrise Daily' na tashar ChannelsTV.

Kunle Olawunmi, wanda yanzu Farfesa na kan lamuran tsaro ya gabatar da hirar ne ranar Laraba, 25 ga Agsuta, 2021.

A cewar PUNCH, yardaddun majiyoyi sun bayyana cewa hukumomin tsaro irinsu DSS da DIA sun alanta neman Olawunmi ruwa a jallo.

Yayinda aka tuntubi Kakakin DIA, Manjo Afolashade Ojolowo, yace yana hutu saboda haka bai da labari.

Kara karanta wannan

Tattaunawa da Ortom: 'Yan jaridan Channels TV sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS

Ana neman tsohon sojan da yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram
Da duminsa: An alanta neman tsohon sojan da yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A riwayar SaharaReporters, hukumar DIA ta bukaci Olawunmi ya kai kansa hedkwatarta dake Abuja ranar Talata da Fasfot dinsa.

Majiyar tace:

"Hukumar ta alanta neman Navy Commodore Kunle Olawunmi (mai ritaya) ruwa a jallo kan fasa kwan da yayi kan masu daukar nauyin Boko Haram dake gwamnatin Buhari."
"Sun ce ya je ofishin DIA dake Abuja ranar Talata tare da Fasfot dinsa na fita kasar waje."

Wace hira yayi da yan jaridan ?

Tsohon Sojan Ruwa, Commodore Kunle Olawunmi, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta san wadanda ke daukan nauyin yan ta'addan Boko Haram da suka addabi kasar.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida a shirin Sunrise Daily na ChannelsTV.

Olawunmi yace:

"Su (gwamnati) sun sani. A Afrilun shekarar nan, gwamnati ta ce ta damke yan kasuwar canji 400 dake daukan nauyin yan Boko Haram. Haka suka fada mana."

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta sammaci yan jaridar ChannelsTV kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja

"Mun san su fa, me zai hana wannan gwamnatin, idan ba siyasa take ba, ta fito da wadannan mutane su gurfana a kotu."

Ya ce gwamnatin tarayya na jan kafa wajen yaki da ta'addanci saboda wasu daga cikin masu daukar nauyin Boko Haram na cikin gwamnatin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel