Hukumar DSS ta sammaci yan jaridar ChannelsTV kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja
- Gwamnati tarayya ta sammaci yan jarida zuwa Abuja
- Wannan ya biyo bayan wasikar tuhumar da hukumar NBC ta aikewa Channels
- Gwamnati na tuhumar ChannelsTV da yunkurin tayar da tarzoma a kasa
Rahotanni na nuna cewa hukumar DSS ta sammaci wasu yan jaridar gidan talabijin ChannelsTV dake Legas kan hirar da sukayi da wani tsohon Soja mai suna, Kunle Olawunmi.
A cewar Arise News, daya daga cikin lauyoyin Channels TV na tare da yan jaridan dake hanyarsu ta zuwa Abuja yanzu haka.
Wani hira yan jaridan sukayi?
A ranar Talata, tsohon Sojan Ruwa, Commodore Kunle Olawunmi, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta san wadanda ke daukan nauyin yan ta'addan Boko Haram da suka addabi kasar.
Ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida a shirin Sunrise Daily na ChannelsTV.
Olawunmi yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Su (gwamnati) sun sani. A Afrilun shekarar nan, gwamnati ta ce ta damke yan kasuwar canji 400 dake daukan nauyin yan Boko Haram. Haka suka fada mana."
NBC Ta Tuhumi Channels TV Kan Tattaunawa da Gwamna Ortom
A bangare guda, hukumar kula da kafafen watsa labarai ta ƙasa (NBC), ta tuhumi Channels tv kan maganganun da Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya yi a shirinta na Sunrise daily ranar Talata.
Hukumar NBC ta bayyana hakane a wata takarda da ta aike wa kafar watsa labaran, kamar yadda punch ta ruwaito.
Takardar tana ɗauke da kwanan watan 24 ga watan Agusta, kuma shugaban hukumar NBC, Balarabe Ilelah, ya saka hannu.
Wasu maganganu Ortom ya yi?
Ortom, wanda ya bayyana a cikin shirin, yace:
"Shugaban ƙasa na sakani tunanin ko abinda ake faɗa kansa cewa yana da wata ɓoyayyar manufa ga ƙasar nan gaskiya ne."
"Saboda komai ya fito fili yana son maida ƙasar nan ta fulani kuma ba shine bafullatani na farko da ya shugabanci kasar nan ba."
Asali: Legit.ng