Ban taba tsammanin haka Ali Nuhu ya iya rawa ba, Jarumar Nollywood ta wallafa bidiyon jarumin

Ban taba tsammanin haka Ali Nuhu ya iya rawa ba, Jarumar Nollywood ta wallafa bidiyon jarumin

  • Jarumai da dama sun kwashi rawa ga wata waka ta fim din jaruma Toyin Abraham, cikin jaruman kuwa har da fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu
  • Mabiyan ta sun bayyana mamakinsu a kan wasu salo iri-iri na rawar Ali Nuhu wadanda suka kayatar kwarai, da dama sun yi mamakin yadda aka yi ya samu wannan kwarewa
  • Kamar yadda aka ga bidiyon jarumin yana cashewarsa cikin salo na kwarewa, ita kanta jaruma Toyin sai da ta bayyana mamakinta a kan rawar

Wata wakar sabon fim din jaruma Toyin Abraham, ‘The Ghost’" ta kayatar da mutane da dama don ‘yan uwanta jarumai sun nuna mata soyayya sosai a kafafen sada zumuntar zamani.

Wakar wacce ta sa abokan sana’ar ta suka yi ta kwasar rawa suna yin bidiyo, cikinsu kuwa ba a bar jarumin Kannywood, Ali Nuhu ba domin sai da ya gwada ta sa bajimtar.

Kara karanta wannan

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

Ban taba tsammanin haka Ali Nuhu ya iya rawa ba, Jarumar Nollywood ta wallafa bidiyon jarumin
Ban taba tsammanin haka Ali Nuhu ya iya rawa ba, Jarumar Nollywood ta wallafa bidiyon jarumin. Hoto daga @toyin_abraham
Asali: Instagram

Mabiyan Toyin kansu sun sha mamaki kwarai a kan rawan burgewar da Ali Nuhu ya kwasa bayan ita da kan ta Toyin ta wallafa bidiyon rawar nasa.

Jarumar Nollywood din ta yi iyakar kokarin ta wurin ganin cewa sabon fim din na ta na The Ghost ya kewaye ko ina a fadin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fitacciyar jarumar wacce tauraron ta ya ke tsaka da haskawa ta saki wakar fim din kuma manyan sanannun abokan sana’ar ta suka dinga kwasar rawa don dai wakar ta kewaye ko ina.

A cikin shirin fim din, Ali Nuhu ya bayyana sannan ya tura wa jarumar bidiyon rawar da ya kwasar wa wakar sannan ta wallafa bidiyon rawar ta sa a shafin ta.

A cikin bidiyon, an ga yadda Ali Nuhu ya zage yana kwasar rawa irin ta zamani cike da burgewa. Har amfani yayi da hannayensa yayi yayin da wakar ta ke tashi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Bayan wallafa wakar, jarumar ta wallafa cewa bata taba tunanin kwarewarsa a rawa ta kai haka ba.

'Yan jaridan Channels TV 2 sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS kan tattaunawar sukar Buhari

A wani labari na daban, jami'an hukumar DSS sun titsiye 'yan jarida 2 na gidan talabijin na Channels masu suna Chamberlain Usoh da Kayode Okikiolu, na tsawon sa'o'i a ranar Alhamis kan tattaunawa da suka yi da Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue wacce suka yi a ranar Talata.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, daga bisani jami'an tsaron na sirri sun sako 'yan jaridan wurin karfe 7 na yamma.

Wani babban jami'i a hukumar ya sanar da Daily Trust cewa, an gayyesu ne sakamakon wani korafi da hukumar watsa labarai ta kasa, NBC ta mika musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel