‘Yan bindiga sun karbi N68m da sababbin babura kafin su fito da ‘Yan Islamiyyan Tegina

‘Yan bindiga sun karbi N68m da sababbin babura kafin su fito da ‘Yan Islamiyyan Tegina

  • Sai da aka kara biyan wasu kudin kafin yaran da aka sace a Tegina su fito
  • Wata majiya tace iyaye da abokan arziki sun yi karo-karon Naira miliyan 18
  • ‘Yan bindigan sun bukaci a kawo masu sababbin babur kafin su saki yaran

Niger - Sauran ‘daliban makarantar Islamiyyar Tanko Salihu da aka dauke a garin Tegina, jihar Neja, sun fito ne bayan an kara wa ‘yan bindiga kudi.

Yadda lamarin ya kasance

Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa sai da aka kara wa ‘yan bindigan kudin fansa bayan sun ki karbar Naira miliyan 50 da aka kai masu a baya.

‘Yanuwa da iyayen wadannan yara sun yi kokarin kara hada Naira miliyan 30 bayan sun biya Naira miliyan 20 domin a ceto yaran a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Mutum miliyan 1 za su amfana, Gwamnati ta maido TraderMoni, MarketMoni, FarmerMoni

Rahoton yace ko da aka je za a ba ‘yan bindigan kudin, sai suka ce an samu gibin Naira miliyan 4.6, suka cigaba da tsare wadannan kananan yaran.

Daga baya an kira iyayen yaran, an nemi su kawo ragowar Naira miliyan 4.6 da kuma cikon Naira miliyan biyu da aka samu a kudin farko da aka kai.

Sai da aka hada wa 'yan bindiga da babur

Duka-duka, ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da yaran sun nemi a kawo karin Naira miliyan 6.6, sannan suka ce a kawo masu sababbin babura shida.

‘Yan bindiga
Babur kirar bajaj a kasuwa Hoto: jiji.ng
Asali: UGC

Majiya ta shaida wa jaridar cewa an yi karo-karo, an hada Naira miliyan 18 domin a bada wadannan tulin kudi, a kuma saye babura kirar ‘Bajaj’.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ana saida irin wannan babur a kan kudi kimanin N300, 000 a kasuwa.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Yan bindiga sun sace Mai takaba kwana 1 da mutuwar Maigidanta a jihar Katsina

Sai bayan an cika wadannan sharuda ne aka fito da yaran. Shugaban makarantar, Alhaji Garba Alhassan, ya tabbatar da cewa sun samu ‘yanci a jiya.

Iyaye sun yi farin-cikin samun labarin dawowar ‘ya ‘yan na su bayan kusan watanni uku a tsare. A yau ake sa ran yaran za su gana da wakilan gwamnati.

Wasu yara sun shiga ha'ula'i

An ji cewa wasu daga cikin yaran makarantar Islamiyya ta Tegina da ‘yan bindiga nsuka yi awon-gaba da su, suna cikin wani mawuyacin hali.

Shugaban makarantar, Abubakar Alhassa ya bayyana cewa yan bindigan sun kira shi domin sanar da shi irin halin da yaran makarantar su ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel