SSS ta musanta tarwatsa taron likitocin da suke shirin shillawa Saudi Arabia aiki

SSS ta musanta tarwatsa taron likitocin da suke shirin shillawa Saudi Arabia aiki

  • Hukumar jami'an tsaron farin kaya ta karyata zantukan da ke yawo na cewa jami'anta sun fatattaki likitoci a otal din Sheraton na Abuja
  • An gano cewa hukumomi daga kasar Saudi Arabia sun dira a Abuja sun kuma tantance likitocin domin ba su aiki a asibitocin
  • Afunanya, mai magana da yawun hukumar DSS ya ce, wannan zancen ba gaskiya bane kuma duk mai hankali ba zai yarda da shi ba

FCT, Abuja - Jami'an tsaron farin kaya sun musanta tarwatsa likitocin da suka halarci taron tantancewa na daukar aiki a kasar Sadi Arabia da aka yi a otal din Sheraton a Abuja a ranar Alhamis.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mai magana da yawun hukumar, Dr Peter Afunanya, ya musanta wannan lamarin ne a wata takarda da ya fitar a Abuja a ranar Juma'a.

SSS ta musanta tarwatsa taron likitocin da suke shirin shillawa Saudi Arabia aiki
SSS ta musanta tarwatsa taron likitocin da suke shirin shillawa Saudi Arabia aiki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Afunanya yace wannan musantawar ta zama dole bayan yada labarin bogi da ake ta yi a wasu kakafen yada labarai kan yadda jami'an DSS suka tarwatsa likitocin.

Duk da babu basira a lamarin kuma labarin bai hadu ba, wani sashi na yada labarai ya ruwaito hakan saboda basu damu da tantance labari ba.
Babu kuma wata shaida da aka hada da ita da za ta tabbatar da cewa jami'an DSS ne suka kaiwa likitocin farmaki a wannan otal din. A bayyane yake cewa an hada labarin ne domin a tozarta hukumar," yace.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, ta ce Afunanya ya yi kira ga kafafen yada labarai da su dinga duba labarai da kyau tare da tantancesu domin gudun sanar da jama'a shirme ko kuma saka halin tsaron kasa a ha'u'la'i.

Hedkwatar tsaro: Idanun masu kula da CCTV ta NDA biyu yayin da aka kai hari

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta kasa, ta ce jami'anta dake kula da CCTV idon su biyu yayin da miyagun 'yan bindiga suka kutsa makarantar horar da hafsoshin soja ta NDA da ke Kaduna.

A take suka kashe hafsoshin soja biyu yayin da suka yi garkuwa da daya sannan suka raunata daya bayan mummunan harin da suka kai a sa'o'in farko na ranar Talata.

TheCable ta ruwaito cewa, an tabbatar da cewa jami'an da ke kula da CCTV na NDA suna sharar baccinsu ne yayin da wannan mummunan harin ya auku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel