Hushpuppi: Tsoro ya mamaye Abba Kyari, ya goge sabon wallafa da yayi a Facebook yayin da IGP ya karbi rahoto

Hushpuppi: Tsoro ya mamaye Abba Kyari, ya goge sabon wallafa da yayi a Facebook yayin da IGP ya karbi rahoto

  • Dakataccen shugaban rundunar IRT, DCP Abba Kyari, na iya sanin makomarsa kan zargin zamba nan ba da dadewa ba
  • Joseph Egbunike, Mataimakin Babban Sufeton 'Yan Sanda ya mika rahoton kwamitin binciken Kyari ga IGP Baba
  • A ranar Alhamis 26 ga watan Agusta Kyari ya sake bayyana a shafin Facebook yan makwanni bayan hutun da ya ba kansa a kafafen sada zumunta

FCT, AbujaMai yiwuwa gabatar da rahoton kwamitin binciken Abba Kyari ga Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba, ya aika babban sako ga jami'in da ke tsaka mai wuya.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Kyari, wanda shine shugaban rundunar IRT kafin dakatar da shi, ya goge sabon sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook sa'o'i bayan IGP Baba ya karbi rahoton.

Hushpuppi: Tsoro ya mamaye Abba Kyari, ya goge sabon wallafa da yayi a Facebook yayin da IGP ya karbi rahoto
Abba Kyari ya goge sabon sakon da ya wallafa a Facebook a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta Hoto: Abba Kyari.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa an ambaci Kyari a cikin damfarar dala miliyan 1.1 wanda ake zargin wani mai tasiri a shafin Instagram, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi da wasu mutane hudu da aiwatarwa.

A cewar rahoton, bayan hutun makwanni uku, Kyari ya dawo shafin zumunta a ranar Alhamis, 26 ga Agusta. Kafin nan, sakonsa na ƙarshe a Facebook ya kasance a ranar 4 ga Agusta, 2021, wanda a nan take ya goge shi sannan ya bace bat.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kammala bincike kan DCP Abba Kyari, IGP ya karbi rahoton

A baya mun kawo cewa an kammala bincike kan zargin da ake yiwa tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari.

Shugaban kwamitin da Sifeto Janar na yan sanda ya nada don binciken, DIG Joseph Egbunike, ya gabatar da kundin sakamakon binciken ga IGP Mohammed Alkali a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, 2021.

Kakakin hukumar yan sanda, CP Frank Mba, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki da yammacin nan a shafin hukumar.

A jawabin, DIG Egbunike ya godewa IGP bisa yarda da kwamitinsa da mambobinta da wannan aiki na bincike mai muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel