Yajin-aiki: Gwamna ya shafe watanni 19 bai biya Likitocin jihar Abia albashi ba Inji NARD

Yajin-aiki: Gwamna ya shafe watanni 19 bai biya Likitocin jihar Abia albashi ba Inji NARD

  • Kungiyar NARD tace akwai Likitocinta da sun yi wata da watanni babu albashi
  • A jihar Abia, NARD ta na zargin gwamna da kin biyan albashin watanni har 19
  • Likitocin da ke yajin-aikin sun ce alawus din hadarin da ake ba su, ya yi kadan

Abia - Kungiyar NARD ta likitocin da ke neman kware wa a kan aiki ta yi Allah-wadai da gwamnatin da Okezie Ikpeazu yake jagoranta a Abia.

Ikpeazu ya saba alkawari

Kamar yadda muka samu rahoto daga gidan talabijin Channels TV a ranar Alhamis, gwamnatin Abia ta shafe watanni 19 ba ta biya likitoci albashi ba.

A wani jawabi da NARD ta fitar a ranar 26 ga watan Agusta, 2021, bayan zaman da majalisar kolin NEC ta yi a garin Benin, ta yi tir da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Kiwon dabbobi: Gwamna ya karyata fadar Shugaban kasa, yace ba a aiko masa da N6bn ba

“Majalisar NEC ta ji takaici, amma ba ta yi mamaki da gwamnan jihar Abia yaki biyan kudin watanni 19 da ‘yan kungiyarmu ke bin shi bashi ba."
“Gwamnan (na Abia) ya yi alkawarin zai biya wadannan kudi ne tun kwanaki 23 da suka wuce.”

Gwamnan jihar Abia
Gwamnan Abia, O. Ikpeazu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Akwai wasu jihohin da likitoci ke wahala?

Haka zalika, kungiyar ta NARD tace likitocinta suna bin gwamnonin Imo, Ekiti da Ondo bashin albashinsu na tsawon watanni goma, shida da kuma hudu.

Takardar bayan taron da NARD ta fitar ya kuma bayyana cewa akwai likitoci 114 da aka yi wata daya zuwa watanni hudu ba tare da sun ci daga guminsu ba.

A game da alawus din da ake ware wa ma’aikatan lafiya saboda yiwuwar aukuwar wani hadari a a asibitoci, NARD tace N5, 000 a duk wata ya yi masu kadan.

Kara karanta wannan

Kotu ta tsare mutane 8 da ake zargi da yin garkuwa da matar kwamishinan Benue

Majalisar NEC ta kungiyar likitocin ta yi wannan magana ne a lokacin da ta ke cikin yajin-aiki.

Jaridar ta rahoto NEC ta na cewa iyalan likitoci 19 da cutar COVID-19 ta kashe ba su iya karbar kudin inshora ba duk da alkawuran da gwamnati ta yi masu.

Kashe-kashe ya yi yawa - Sultan

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bada labarin yadda aka birne gawawaki kusan 80 a rana daya a garin Sokoto kwanakin baya.

Duk da kashe-kashen da aka yu, Sarkin Musulmi ba ya goyon bayan gwamnati ta nemi ceton kasashen waje, ya yi kira ga hukuma ta kawo karshen lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel