Za a je kotu da PDP, APC idan ba a tsaida Ibo a matsayin 'Dan takarar Shugaban kasa ba
- Wasu kungiyoyi sun huro wuta a kan sai ‘Dan kudu maso gabas ne zai yi takara a 2023
- Daga ciki akwai 'Southeast for President and Igbo Leadership Development Foundation'
- Kungiyoyin sun ce za su je kotu idan har jam’iyyu suka hana ‘YIbo tikitin shugaban kasa
Kungiyar Southeast for President and Igbo Leadership Development Foundation ta dage a kan sai an ba Ibo tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Dole a ba Ibo takara - Kungiyoyi
Wannan kungiya da ke goyon-bayan ‘yan siyasan kasar Ibo ta ce za ta kai karar APC da PDP da sauran jam’iyyun siyasan kasar idan ba ayi adalci ba.
Southeast for President and Igbo Leadership Development Foundation ta na so jam’iyyun su yi la’akari da tsarin karba-karba wajen fitar da ‘dan takara.
Punch ta rahoto kungiyar tana neman a tsaida ‘dan takarar shugaban kasa daga kudu maso gabas.
Shugaban kungiyar SEFORP na kasa, Okechukwu Obioha da takwaransa na ILDF, Godwin Udibe sun kira taron ‘yan jarida a kan wannan batu a Enugu.
Da suke magana da ‘yan jarida a ranar Laraba, Obioha da Udibe sun ba da jam’iyyun wa'adin kwanaki 30 su biya masu bukatunsu, ko a shiga shari’a.
Me za ayi idan aka hana Ibo tikiti?
Godwin Udibe ya yi magana a madadin kungiyoyin, yace sun ga ana nema ayi masu sakiyar da ba ruwa.
“Mun lura da wasu makarkashiya da dabaru da jam’iyyun siyasa suke yi na danne kudu maso gabas a takarar shugaban kasar da za ayi a zaben 2023.”
“Muna so mu yi bayani da kyau cewa duk wani shiri da za ayi a matakin jam’iyya ko a siyasance da zai hana Ibo tuta a 2023 zai gamu da kara a kotu.”
Udibe yace su yi iya karfinsu domin ganin an bi karba-karba da dokar kasa. Bayan kwana 30 za su nemi kotu ta wajabta wa jam'iyyun tsaida ‘dan Kudu maso gabas.
Ortom ya soki mulkin APC
Gwamna Samuel Ortom yace masu rike da madafan iko sun haramta masa ganin shugaba Muhammadu Buhari, yace an yi masa shamaki a fadar Shugaban kasa.
Da aka yi hira da shi a makon nan, Samuel Ortom yace an daina sauraronsa, kuma jihohin APC kadai gwamnatin Muhammadu Buhari ta ke ba aron kudi a yanzu.
Asali: Legit.ng