Matasa sun jibge gawawwakin mutane 20 da aka kashe a gaban gidan Gwamnati a Jos

Matasa sun jibge gawawwakin mutane 20 da aka kashe a gaban gidan Gwamnati a Jos

  1. Kashe-kashen Jos ya dauki wani salo bayan an kai hari a Yelwan Zangam
  2. An kashe mutane sama da 35 a cikin makon nan a kauyen Yelwan Zangam
  3. Matasa sun yi zanga-zanga, sun kai gawawaki har gaban gidan gwamnati

Jos - Gawawwaki fiye da 20 aka ajiye a kofar shiga gidan gwamnatin jihar Filato da ke Little Rayfield bayan harin da aka kai a Yelwan Zangam, garin Jos.

Daily Trust ta rahoto cewa daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a babban birni Jos, sakamakon harin da aka kai wa mutanen Anaguta a kauyen Yelwan Zangam.

A ranar Talata cikin dare aka auka wa ‘yan kabilar Anaguta da ke zaune a kauyukan da ke wajen Jos. Wannan harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 40.

An kai wa 'Yan Majalisa da Gwamna gawawwaki

Mutanen kauyen na Yelwan Zangam sun ajiye gawawwakin mutanen da aka hallaka a asibitin Filato. Daga baya wasu matasa sun je asibitin, sun fito da gawan.

Rahoton yace fusatattun matasan sun dauki gawar mutanen, sun zuba a cikin mota, suka wuce da su zuwa gaban majalisar dokokin jihar da ke kusa da wurin.

Daga nan kuma matasan suka sake daukar gawan, suka shimfida su a gidan gwamna a Little Rayfield.

Matasa a Jos
Masu zanga-zanga tare da Ayuba Aboke Izam Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Masu zanga-zangar sun nuna wa Duniya mutanensu da aka kashe. A cikin wadanda aka kashe a sabon harin da aka sake kai wa akwai maza, mata da kananan yara.

Shugaban majalisar dokokin jihar Filato, Rt. Hon. Ayuba Aboke Izam ya hadu da masu zanga-zangar.

Wanene suka kai wannan hari?

Wasu daga cikin mazauna garin Yelwan Zangam suna ganin makiyaya ne suka auka masu, suka kona gidaje da motocin jama’a, sannan suka kashe mutane 37.

Shugaban kungiyar Gan Allah Fulani Development Association of Nigeria, GAFDAN na Filato, Garba Abdullahi Muhammed, yace ba Fulani suka kai harin ba.

Ba yanzu aka fara ba

Bayan an hallaka wasu matafiya a Gada-biyu, an ji mutanen kabilar Irigwe suna cewa an kai masu hari inda aka hallaka mutane biyar a yankin garin Bassa.

Shugaban kungiyar mutanen Irigwe yace an kashe masu mutane a lokacin da ake kulle. Baya ga haka, wasu sun bace bayan harin da aka kai a Dong da Tafi-Gana

Asali: Legit.ng

Online view pixel