Budurwa ta sanar da yadda saurayi ya fara surkullen tsafi yayin da ya ke kokarin cewa ya na son ta

Budurwa ta sanar da yadda saurayi ya fara surkullen tsafi yayin da ya ke kokarin cewa ya na son ta

  • Wata budurwa ta bayyana yadda wani saurayi ya biyo ta a titi yana surkullen tsafi
  • Ta bayyana yadda bayan ya kammala surkullen ya bukaci ta bi shi amma ta fara addu’a
  • Bayan ta daina bin shi sai ya bi ta da gudu har sai da suka kai idon mutane tukunna ya dakata

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook kan yadda wani mutum ya fara surkullen tsafi bayan ya ganta a titi yana kuma son ya bayyana mata soyayyarsa.

Morenikeji Adekunle Praiseberry, ta bayyana yadda ta bar diyar ta da kakar ta a gida lokacin da ta fita ciro kudi a banki, tace kawai ta ji wani yana bin ta kamar yana so yayi mata magana yana ta kusantar ta, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kara karanta wannan

Najeriya Dadi: Baturiya ta yi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta

Budurwa ta sanar da yadda saurayi ya fara surkullen tsafi yayin da ya ke kokarin cewa ya na son ta
Budurwa ta sanar da yadda saurayi ya fara surkullen tsafi yayin da ya ke kokarin cewa ya na son ta. Hoto daga Lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Ta ce ta ji lokacin da yake ta surkullen tsafi sannan ya umarce ta da ta bishi, tana jin tana son bin shi amma sai ta tuna ba ta san shi ba, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Ta kara da bayyana yadda ta ki bin shi ta fara addu’o’i tana tsere wa daga inda ya ke. Ta cigaba da bayyana yadda mutumin ya bi ta da gudu har sai da ta isa wani gida inda jama’a suke.

Kamar yadda ta wallafa:

Ku taya ni godiya ga Ubangiji. Na fita zan je ciro kudi saboda ba ni da ko sisi a jiki na. Ire yana bacci shiyasa ban zo da shi ba. Muna waya da kakata ta na min addu’o’i.
Kawai sai ga wani mutum nan ya zo yana so yayi min magana a kan titi duk da dare ya tsala. Sai nace wa kaka ta zan kira ta anjima. Take a nan ya fara surkullen tsafi sai ya umarce ni da in bishi, sai na ji ina son in bi shi, har na fara bin shi kawai sai hankali na ya dawo jiki na.

Kara karanta wannan

Ba dukkan tubabbun 'yan Boko Haram bane 'yan ta'adda, Gwamna Zulum

Sai na dakata na fara addu’o’i na fara gudu sai ya fara bi na da gudu har sai da muka isa cikin mutane tukunna ya dakata.

Gidaje 5 na hafsoshin soja 'yan bindiga suka balle a NDA Kaduna

A wani labari na daban, ‘yan bindigan da suka shiga barikin Afaka da ke NDA a jihar Kaduna ranar Talata sun fada wa gidaje 5 da ke makwabtaka da juna ne. An samu wannan bayanin ne a wata takarda wacce Daily Trust ta gani.

Kamar yadda jami’an binciken sirri suka bayyana, ‘yan bindigan sun ci karensu babu babbaka saboda sojojin ba su yi gaggawar zabura ba a kan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel