'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 3 yayin da suka kai musu farmaki kan hanyarsu ta kai masu laifi gidan yari

'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 3 yayin da suka kai musu farmaki kan hanyarsu ta kai masu laifi gidan yari

  • Rudunar ‘yan sandar jihar Osun ta ce ta sheke mutane 3 ya yin musayar wutar da ta shiga tsakaninsu a jihar
  • Dama wadanda ake zargin sun kai wa motar ‘yan sandan farmaki kamar yadda ‘yan sandan suka tabbatar
  • Lamarin ya faru a titin Osogbo-Ilesa bayan rafin Osunjela a ranar 25 ga watan Augustan 2021 da misalin 3:30pm

Osun - Hukumar ‘yan sanda na jihar Osun ta ce sun samu nasarar sheke wasu da ake zargin makasa ne yayin musayar wutar da ta auku tsakaninsu bayan sun kai wa motar ‘yan sandan farmaki.

TheCable ta ruwaito cewa, kamar yadda ‘yan sandan suka tabbatar, an kai wa abin hawansu hari ne a ranar Laraba a kan titin Osogbo zuwa Ilesa bayan rafin Osunjela.

'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 3 yayin da suka kai musu farmaki kan hanyarsu ta kai masu laifi gidan yari
'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 3 yayin da suka kai musu farmaki kan hanyarsu ta kai masu laifi gidan yari. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

‘Yan sandan sun ce suna tafe da wadanda ake zargin ne daidai Ilesa domin mika su gidan gyara hali amma sai motarsu ta lalace.

Ana tsaka da gyaran ne sai ga wasu ‘yan bindiga guda 4 a babura suka kai musu farmaki suna kokarin ceton wadanda ake zargin makasan ne, TheCable ta ruwaito.

Harin wanda ya kai ga musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindiga, ya yi sanadiyyar ajalin mutane 3 daga cikin ‘yan bindigan.

Ranar 25 ga watan Augustan 2021 da misalin 3:30pm, ‘yan sanda suna tafe da wasu da ake zargin makasa ne za su kai su gidan gyaran halin Ilesa, bayan rafin Osunjela wuraren titin Osogbo da ke Ilesa, sai motar ta samu matsala, a cewar Opalola Yemisi, kakakin hukumar ‘yan sanda kamar yadda takardar ta zo.
Wasu kanikawa suna tsaka da gyaran motocin ne sai ga ‘yan bindiga 4 daga titin Osunjela a babura kirar Bajaj inda suka kai wa ‘yan sandan farmaki suna harbe-harbe.

Bayan sun sha ragargaza daga wurin ‘yan sandan suka tsere suka suka bar baburansu da bindigogin toka 3, adduna da sauran miyagun makamai.

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

A wani labari na daban, an kama mutane 10 da suke da alaka da kai sabon hari kauyen Yelwa Zangam na Jos ta arewa da ke jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Gwamna Simon Lalong ya kwatanta harin a matsayin rashin imani, sannan ya shirya taro na gaggawa don tattaunawa da kuma neman hanyar kawo garanbawul ga kashe-kashen da aka maimaita a jiharsa.

A wata takarda wacce darektan watsa labarai ya saki, Makut Mechan, ya ce gwamnan ya umarci jami’an tsaro su binciko duk wadanda suke da hannu a lamarin da masu daukar nauyinsu don a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel