Za a fara kera jiragen sama a kasar nan kafin Buhari ya bar kan mulki inji Minista

Za a fara kera jiragen sama a kasar nan kafin Buhari ya bar kan mulki inji Minista

  • Hadi Sirika ya ziyarci kamfanin Magnus aircraft manufacturing industry a Hungary
  • Ministan yace za a kulla yarjejeniya domin a rika kera jiragen sama a nan Najeriya
  • Ana sa rai idan wannan magana ta tabbata, a samu kamfanin kere-kere nan da 2023

Kafin karshen 2023, Najeriya za ta zama cikin kasashen da ake kera jiragen sama a Duniya.

Rahoton da Tribune ta fitar yace gwamnatin tarayya ta shiga wata yarjejeniya da wani kamfani a kasar Hungary da ya yi fice wajen kere-keren jirage.

Yarjejeniya da Magnus aircraft manufacturing industry

Ministan harkokin jirgin sama na kasa, Hadi Sirika yace hada-kai da kamfanin Magnus aircraft manufacturing industry zai sa a iya kera jirgi a Najeriya.

Jaridar ta rahoto Ministan yana wannan bayani ne a lokacin da ya ziyarci Magnus aircraft manufacturing industry a birnin Pogany, kasar Hungary.

Kara karanta wannan

Hoton tsohon soja mai shekaru 96, ƴaƴa 50 da mata takwas da ke safarar wiwi tsawon shekaru 39 a Niger

Sanata Hadi Sirika yace kafin wa’adin Muhammadu Buhari ya cika, za a fara kera jiragen sama a gida. A watan Mayun 2023 ne Buhari zai bar kujerar mulki.

“Idan muka hada-kai da su, za mu kafa kamfanin kere-kere, mu fara kera wa daga baya.”

Jiragen sama
Jiragen sama Hoto: www.bloomberg.com
Asali: UGC

Meyasa jiragen kamfanin Magnus suka yi suna?

Sirika yace jiragen kamfanin Magnus aircraft suna da kyau sosai wajen aikin sojoji, domin jiragensu suna iya juya wa a saman iska saboda rashin nauyi.

Jawabin da Ministan ya yi a kasar wajen ya fito ne ta bakin James Odaudu inda aka ji yana cewa ana amfani da jiragen wajen kai hari, wasanni da nishadi.

Mai girma Ministan yace abin da ya ba shi sha’awa da wadannan jirage shi ne suna amfani ne da man fetur, kuma babu jiragen yakin da suka fi su nagarta.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman FEC na farko, ya amince a sayo karnukan N650m

Kafin a kai ga fara kera jirage a Najeriyan, Ministan zai duba yanayin kasuwar da ake ciki, da kuma ganin-daman gwamnati na shiga wannan yarjejeniya.

Idan hakan ta tabbata, Najeriya za ta yi zarra a harkar jirgin sama, kuma za a rika zuwa daga kasashen da ke makwabtaka domin kula da gyaran jirage.

Da walakin a harin NDA - Buhari

Fadar Shugaban kasa ta yi magana a kan harin da aka kai a makarantar sojoji ta NDA. Garba Shehu ya ce bai cire siyasa ba domin komai na iya faru wa.

Hadimin Shugaban kasar yana mamakin harin da aka kai a lokacin da sojoji ke galaba a kan 'yan ta'adda, yace watakila ana neman bata sunan gwamnati ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel