Operation Hadin Kai: Dakarun soji sun cafke mai samarwa Boko Haram da takin gona

Operation Hadin Kai: Dakarun soji sun cafke mai samarwa Boko Haram da takin gona

  • Rundunar sojin kasa na shashi na biyu na JTF na arewa maso yamma sun damki wani Yusuf Saleh
  • Ana zarginsa da kai wa ‘yan Boko Haram takin Urea a kauyen Bayamari da ke karamar hukumar Geidam da ke jihar Yobe
  • Dama gwamnati ta hana siyar da takin Urea domin ‘yan ta’adda suna amfani da shi wurin hada abubuwa masu fashewa

Geidam, Yobe - Rundunar sojin kasa ta sashi na biyu ta JTF a arewa maso gabas ta Operation Hadin Kai ta kama wani Yusuf Saleh, bisa zargin siyar wa da ‘yan Boko Haram din kauyen Bayamari da ke karamar hukumar Geidam da ke jihar Yobe.

‘Yan sa kai ne suka kama shi bayan samun gamsassun labarai a kansa. An samu buhunhuna 38 masu cikin 50kg daga hannunsa na takin Urea, HQ Nigerian Army ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Operation Hadin Kai: Dakarun soji sun cafke mai samarwa Boko Haram da takin gona
Operation Hadin Kai: Dakarun soji sun cafke mai samarwa Boko Haram da takin gona. Hoto daga HQ Nigerisn Army
Asali: Facebook

Dama gwamnati ta hana sayar da takin Urea saboda ‘yan ta’adda suna amfani da shi wurin hada abubuwa masu fashewa. Yanzu haka ana ta samun labarai masu amfani daga bakinsa.

Rundunar OPK sun yaba wa kokarinsu inda suka yi gaggawar kama wanda ake zargin. Sannan sun bukaci a dinga bin diddikin duk wasu labarai a kan ‘yan ta’addan don mutane da dama sun wahala a hannunsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tabbatar wa da mazauna yankin arewa maso gabas masu bin doka cewa shugaban sojin kasa ya daura dammarar kawo karshen Boko Haram da ISWAP a maboyarsu. An shawarci mazauna yankin arewa maso gabas da su cigaba da kawo labarai wadanda za su taimaka wurin sanin tushen duk wani ta’addanci a yankin.

Yadda aka tsige kakakin majalisa da mataimakinsa a jihar Kebbi

A wani labari na daban, sabbin labarai sun bayyana na yadda majalisar jihar Kebbi ta tsige kakakinta Ismaila Abdulmumuni Kamba da mataimakinsa, Buhari Aliero.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

Daily Trust ta ruwaito cewa, da safiyar Talata ne aka shiga har ofishin kakakin majalisar inda aka sace sandar majalisa wacce ita ce alamar karfin ikon majalisar.

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa sauran 'yan majalisar sun dauke sandar ne domin tabbatar da tsige manyan majalisar. Daga nan ne suka zauna bayan dauke sandar a can wani wuri da ba a sani ba inda suka tsige shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng