Kullum sai an kai hari kananan hukumomin Katsina 10, Aminu Bello Masari
- Gwamna Masari ya karbi bakuncin babban hafsan sojin kasa
- Faruk Yahaya ya kai ziyara Katsina don ganawa da hafsoshin sa
- Masari yace ba ya jin dadin mulkin jihar saboda annobar rashin tsaro
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari yace kananan hukumomi 10 cikin 34 na jihar na fuskantar munanan hare-hare kulli yaumin daga wajen yan bindiga.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin babban hafson soji, Lt Janar Faruk Yahaya, a ranar Alhamis, rahoton DN.
Ya bayyanawa Faruk Yahya cewa yan bindiga na sace mutane, suna jikkata wasu, suna kona gidaje, su yiwa mata fyade kuma su kora Shanu.
A cewarsa, gwamnatin jihar ba ta jin dadin halin rashin tsaron da jihar ke fama kuma saboda haka wajibi ne a kawo
karshen hakan.
Yace:
"A nan jihar Katsina, mun samar da matakai uku na tsaro, daga unguwa-unguwa, zuwa kananan hukumomi, zuwa jiha, domin samar da zama lafiya."
"Muna son zaman lafiya ya dawo da wuri kuma Sojoji su koma bariki domin yan sanda su cigaba da aikinsu."
Gwamnan ya tabbatarwa shugaban Soji cewa gwamnatinsa za ta baiwa hukumar Soji dukkan goyon bayan da take bukata.
Masari: Ba na farin ciki da mulkin Katsina saboda rashin tsaro
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce ba ya jin dadin mulkin jihar saboda annobar rashin tsaro.
Mista Masari, wanda ya yi magana a ranar Juma'a a wata hira da aka yi da shi, ya ce yanayin tsaro na jiharsa na hana shi bacci.
Ya ce:
“A cikin wannan mawuyacin lokaci da rashin tabbas, lamarin tsaro duk ya mamaye batun shugabanci daga safe zuwa dare. Ina samun rahotannin tsaro a kowane lokaci ta hanyoyi da yawa a kullum."
Asali: Legit.ng