Jos ta cika ta banbatse sakamakon rasuwar Attajiri, Alhaji Sama'ila Mai Block
- Allah ya yiwa Attajiri Alhaji Sama'ila Mai Block rasuwa
- Daruruwan mutane sun cika Jos domin halartan Sallar Jana'izar marigayin
- Mutane da dama sun fadi shaidun alkhairi kan marigayi bisa taimakon al'umma da yayi
Plateau - Garin Jos a ranar Talata ta cika ta banbatse da jama'a masu halartar jana'iza sakamakon rasuwar shahrarren attajirii, Alhaji Sama’ila Mohammed, wanda aka fi sani da Mai Block.
Shahrarren Malaman Addini, ma'aikatan gwamnati, yan siyasa, yan'uwa da abokan arziki a dubunsu sun cika gidan marigayin dake bayan tashar motar Jos-Bauchi.
Bayan Sallar Jana'izar, dubunnan jama'an sun raka marigayin zuwa makwancinsa inda aka kwashe awanni biyu kan hanya saboda yawan jama'a. Sai da yan agaji suka bada gudummuwa wajen bude hanya.
A cewar wata majiya, Marigayi Alhaji A S Mohammed ya rasu yana mai shekara 90 a dubiya bayan doguwar rashin lafiya.
Ya rasu ya bar mata uku, yara 38 da jikokin barkatai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya shahara da taimakon jama'a
Marigayin ya shahara da bada taimako da tallafi ga al'ummar yankinsa tsawon shekaru 30 wajen ilimi, addini, marasa galihu, da kiwon lafiya.
Daya daga cikin 'yayansa, Sadis A.S Mohammed, ya bayyanawa DailyTrust yace mutuwar mahaifinsa ya girgiza iyalin da makwabta gaba daya saboda irin halayensa na kwarai.
Yace:
"Duk lokacin da ya hadu da shi, zaka sameshi da murmushi kuma zai maka addu'an albarka da shiriya."
"Mutuwar mahaifinmu ya jefamu cikin jimimai, amma muna farin ciki da abubuwa guda biyu. Na farko shaidun alkhairi da daruruwan mutane ke masa na taimakon da ya musu."
"Na biyu kuma adadin mutanen da suka halarci jana'izarsa da kuam suka rakasa makwancinsa."
An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos
A bangare guda, an ruwaito cewa an kashe mutane da dama a garin Yelwan Zangam da ke karamar hukumar Jos ta Arewa na Jihar Plateau.
Daily Trust ta ruwaito cewa an kuma kone gidaje masu yawa yayin harin.
Wannan na zuwa ne kimanin sati daya bayan kashe matafiya 27 a hanyar Gaba-biyu-Rukuba a karamar hukumar Jos din ta Arewa.
Asali: Legit.ng