Ba sanya: Mazauna Bichi sun fara sammakon zuwa fadar Sarki domin daurin auren ‘yarsa da dan Shugaban kasa

Ba sanya: Mazauna Bichi sun fara sammakon zuwa fadar Sarki domin daurin auren ‘yarsa da dan Shugaban kasa

  • Duk da tarin jami’an tsaron da aka girke, mutanen garin Bichi sun fara yin dafifi zuwa Fadar Sarkin garin domin halartar daurin auren ’yar Sarkin garin
  • Tun da misalin karfe 6:00 na safe mutanen garin suka fara isa wajen daurin auren saboda ba sa so a basu labari
  • Nan da 'yan sa'o'i kadan za a shafa fatiha tsakanin Yusuf, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

Bichi, jihar Kano - Kasancewar jami'an tsaro a Bichi, daya daga cikin sabbin masarautun da aka kirkiro a Kano, bai hana wasu mazauna garin da suka yi cincirindo a fadar Sarkin ba don bikin 'yarsa.

Zahra, daya daga cikin yaran sarkin, za ta auri Yusuf, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin 'yan awanni kadan daga yanzu.

Kara karanta wannan

Sarauta ta hadu da mulki, za a daura auren Yusuf Buhari da Gimbiyar Kano a yau

Ba sanya: Mazauna Bichi sun yi sammakon zuwa fadar Sarki domin daurin auren ‘yarsa da dan Shugaban kasa
Mazauna Bichi sun yi tururuwan zuwa fadar Sarki domin daurin auren ‘yarsa da dan Shugaban kasa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An shirya gudanar da daurin auren ne a babban masallacin Bichi.

Jaridar Daily ta ruwaito cewa a lokacin da wakilanta suka isa garin, wanda ke da tazarar kilomita 30 daga birnin Kano, wasu mazauna garin sun ce sun isa wajen tun da misalin karfe 6:00 na safe saboda ba sa son a yi wani abu babu su a taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta kuma lura da yadda aka jibge jami’an tsaro a cikin garin tare da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a kewayen babban masallacin.

An kuma ga jami’an rundunar 'yan sandan Najeriya a wurare daban-daban inda motocin su da dama ke sintiri yayin da wasu manyan mutane ke isowa.

A cikin birnin na Kano, an tattaro cewa akwai jami’an ‘yan sanda da jami’an NSCDC a kusan dukkan mahada da shataletalen da suka mamaye cibiyar kasuwancin kasar.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abinci dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli

Daya daga cikin manyan hanyoyin da aka tsaurara tsaro a cikin birnin Kano ita ce hanyar Katsina, hanya ɗaya tilo da ke zuwa garin Bichi daga birnin Kano.

Abun da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano wacce ta sace zuciyar da namiji daya tilo da Buhari ya mallaka

Zarah Ado Bayero 'ya ce ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero mai shekara 20, wanda shi ne na hudu a ‘ya’yan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Baya ga kasancewarsa Sarki, mahaifinta shi ne kuma shugaban kamfanin 9mobile. Shi ne ɗan fari da aka haifa a gidan masarautar Kano da ake kira Gidan Dabo.

Ya kasance hakimin kananan hukumomin Fagge, Tarauni da Nassarawa kafin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta nada shi a matsayin sarki mai daraja na daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng