Tsohon shugaban Nigeria ya yi hasashen wani abin mamaki da zai faru a kasar kafin ƙarshen shekarar 2021

Tsohon shugaban Nigeria ya yi hasashen wani abin mamaki da zai faru a kasar kafin ƙarshen shekarar 2021

  • Tsohon shugaban Nigeria na mulkin soja, Yakubu Gowon ya jagoranci masu yi wa kasa addu'a domin neman taimakon Allah da cigaban Nigeria
  • Gowon ya yi bayanin abin da yasa ya ke da muhimmanci yan Nigeria su nemi taimako daga Allah bisa matsalar da kasar ke ciki
  • Nigeria ta kasance tana fama da kallubale daban-daban a sassanta da suka hada da yan ta'adda, masu garkuwa, masu tada kayan baya da sauransu

Legas, Nigeria - Tattalin arzikin Nigeria zai yi farfadowa mai ban mamaki idan hasashen da tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya zama gaskiya.

Tsohon shugaban na Nigeria ya yi hasashen cewa kasar za ta samu waraka kafin karshen shekarar 2021.

Tsohon shugaban Nigeria ya yi hasashen wani abin mamaki da zai faru a kasar kafin ƙarshen shekarar 2021
Tsohon shugaban Nigeria na mulkin soja, Yakubu Gowon. Hoto: General Yakubu Gowon Youth Movement
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar The Nation, Gowon ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nigeria zai samu cigaba sosai, har ta kai ga cewa gwamnatin tarayya ta dena karbo bashi daga kasashen waje.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Ya yi wannan hasashen ne a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta, a yayin da ya jagoranci masu addu'a na Nigeria Prays Mission don yin addu'ar neman Allah ya magance kallubalen tsaro da tattalin arziki na kasar.

Gowon wanda ya yi magana da hanyar amfani da fashar intanet mai bidiyo da sauti ya bukaci yan Nigeria su yi addu'ar Allah ya tabbatar da tsarinsa ga Nigeria cikin gaggawa, The Cable ta ruwaito.

Ya ce:

"Hasashen da ake yi na cewa Nigeria na cikin kasashen duniya biyar da Allah zai yi amfani da su don dawo da duniya kan turbar cigaba ya fara nunawa a yanzu.
"Wani shaida da ke nuni da hakan shine yadda mutane kalilan ne suka rasu sakamakon annobar Coronavirus a kasar idan aka kwatanta da yadda cutar ta yi barna a wasu kasashen duniya."

Tsohon shugaban kasar ya ce zaman lafiyar Nigeria shine abin da ya sa a gaba ya ke kuma roko daga Allah.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya yi addu'ar Allah ya ɗauki ransa: Na ga uku, bana addu'ar ganin Olu na Warri na huɗu

Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Edo ta ce za ta saka tsauraran matakai a bankuna, majami'u, masallatai da wuraren shagulgulan biki kan duk wanda bai nuna shaidar yin riga-kafin cutar korona ba daga watan Satumba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamna Godwin Obaseki na jihar ya sanar da hakan ranar Litinin yayin kaddamar da kashi biyu na riga-kafin cutar korona a Benin City.

Ya ce cutar korona nau'in Delta na yaduwa sosai kuma tana cigaba da yaduwa a kowanne lokaci, lamarin da yasa dole jama'a su yi riga-kafin cutar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164