Sarkin Musulmi Sa'ad III ya cika shekara 65 a Duniya, Buhari ya aika masa sakon musamman

Sarkin Musulmi Sa'ad III ya cika shekara 65 a Duniya, Buhari ya aika masa sakon musamman

  • Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya cika shekaru 65 a yau
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi, inda ya taya sa murna
  • Buhari yace Sultan ya taka rawar gani wajen kawo zaman lafiya da hadin-kai

Abuja - This Day ta ce Muhammadu Buhari ya taya Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, murna yayin da ya kara shekara a Duniya.

Garba Shehu ya fitar da jawabi

Jaridar ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta, 2021, ta hannun mai magana da yawun bakinsa, Garba Shehu.

Da yake magana a jawabin na sa, shugaban kasar ya taya Sultan na Sokoto murnar shafe kusan shekaru 15 a kan karaga, ya na jagorantar al’ummar musulmai.

Muhammadu Buhari ya taya fadar Sarkin Musulmai da masarauta, ‘yanuwa, da jagororin addini, murnar zagayowar ranar da aka haifi Alhaji Sa’ad Abubakar III.

Kara karanta wannan

Hotunan ziyarar Shehu Dahiru Usman Bauchi zuwa fadar shugaba Buhari

A cewar shugaban kasar, Sa’ad Abubakar III ya na tsaya wa adalci da gaskiya a duk inda ya same su.

Mai girma Buhari, ya yaba da irin rawar da Sarkin Musulmin yake taka wa a matsayinsa na uba, tare da tsaya wa marasa karfi da marasa galihu a fadin kasar nan.

Sarkin Musulmi Sa'ad III
Buhari, Sultan, Ooni da sauran Sarakuna Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban Najeriya ya yaba wa Sultan Sa'ad III

Jawabin da aka fitar ya yabi Mai alfarma Sultan a kan yadda ya hada-kai da sauran shugabannin addini a majalisar NIREC wajen kawo zaman lafiya da hadin-kai.

Mai alfarma Sultan, shi ne yake rike da kujerar shugaban majalisar kolin addinin musulunci na kasa, watau Nigeria Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA)

Har ila yau, Muhammadu Sa’ad Abubakar III wanda shi ne Sarkin Musulmi na 20 a tarihi, shi ne shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam mai hedikwata a Kaduna.

Kara karanta wannan

Kwarewa ya kamata a duba wajen tantance wanda zai gaji Buhari, in ji Yahaya Bello

A karshe Buhari ya yi wa shugaban addu’a yayin da ya cika 65 a ranar Talata, yace yana amfani da kwarewarsa na aikin soja da jakadanci wajen yi wa jama’a hidima.

Ana daukar nauyin 'Yan Boko Haram a boye

Wani binciken sirri ya nuna tubabbun cewa tsofaffin ‘Yan Boko Haram suna samu sabuwar rayuwa bayan sun ajiye makamai, sun hakura da fada a Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, gwamnatin Najeriya ta tsara yadda ‘yan ta’adda suke ajiye makamai, sannan tana ba su gidaje da kudi domin a daina yakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel