Najeriya na iya fadawa cikin halin karancin abinci, Ministan Buhari

Najeriya na iya fadawa cikin halin karancin abinci, Ministan Buhari

  • Karamin Ministan noma ya bayyana halin da Najeriya ke ciki game da abinci
  • Shi kuwa Ministan Noma, Nanono, yace akwai bakar talauci a Najeriya
  • An gudanar da taron ciyar da Najeriya a Abuja ranar Litinin

Abuja - Karamin ministan noma da raya karkara, Mustapha Shehuri, ya bayyana cewa Najeriya ka iya fadawa halin karancin abinci saboda babu tsari mai karfi na tsaron abinci.

Shehuri ya bayyana hakan ranar Litinin a 'Taron Ciyar Da Najeriya' da akayi a birnin tarayya Abuja. rahoton TheCable.

Shehuri, wanda ya samu wakilcin Dirakta a ma'aikatar noma, Karima Babangida, ya bayyana cewa wannan taro zai taimakawa ma'aikatar wajen sake duba raunin tsarin abinci a Najeriya don karfafashi.

Yace ma'aikatar shirye take da samar da sabon tsarin tsaron abinci da zai tabbatar cewa dukkan yan Najeriya zasu samu abinci kuma mai inganci.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da tsohon sanatan Najeriya ya mutu

Yace:

"Wannan shine dalilin da yasa ake shirye-shirye daban-daban na tsaron abinci a ma'aikatar a sassan Najeriya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace idan ana son a samu tsari mai inganci, wajibi ne Najeriya ta shawo kan matsalar yunwa, samar da ingantattun abinci da kuma daina asarar abinci.

Najeriya na iya fadawa cikin halin karancin abinci, Ministan Buhari
Najeriya na iya fadawa cikin halin karancin abinci, Ministan Buhari Hoto: Kayan Abinci

Mutane na cikin halin talauci a Najeriya

Duk a taron, Ministan Noma, Muhammad Sani Nanono, ya ce ko Najeriya ta samar da isasshen kayan abinci, wajibi ne wasu su kwana cikin yunwa saboda basu da kudin sayen abinci.

Nanono yace wannan matsalar rashin aikin yi ne kuma babban kalubale ga kasar nan.

Yace:

"Idan bamu mayar da hankali kan wannan babbar matsalar rashin aikin yi cikin matasa da kuma sama musu aikin yi ba, babu abinda mukeyi."

Tsadar abinci: Dalilin da yasa 'yan Najeriya za su ci gaba da cin bakar wahala, in ji masana

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa Sarkin Kano bai halarci daurin auren Yusuf da Zahra ba, Kachallan Kano

Masana tattalin arziki a Najeriya na gargadin cewa zai yi matukar wuya a iya cimma hasashen nan da babban bankin kasar CBN ya yi na sa ran saukar farashin kayayyaki.

Babban bankin ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2022, farashin kayan abinci zai sauka da 10% cikin 100%, saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da kuma rashin bin matakan da suka kamata.

Kasimu Garba Kurfi, wani masanin tattalin arziki da ke birnin Legas, yana cikin masu irin wannan ra'ayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel