Takarar 2023: Cacar baki ta kaure tsakanin Magoya bayan Yahaya Bello da na Bola Tinubu

Takarar 2023: Cacar baki ta kaure tsakanin Magoya bayan Yahaya Bello da na Bola Tinubu

  • Kungiyar Governor Yahaya Bello to President Yahaya Bello ta yi wa TSG martani
  • Hakan na zuwa ne bayan kungiyar TSG ta yi wa Gwamnan jihar Kogi kaca-kaca
  • Gwamna Bello ya fara cewa ya kamata Bola Tinubu ya yafe takara a zaben 2023

Kogi – Bayan jawabin da shugaban kungiyar Tinubu Support Group (TSG), Umar Ibrahim ya yi, magoya bayan Yahaya Bello sun sake jefo da martani.

Governor Yahaya Bello to President Yahaya Bello ta yi magana

Darekta Janar na kungiyar Governor Yahaya Bello to President Yahaya Bello (GYB2PYB) support group, Oladele John Nihi ya yi wa shugaban TSG raddi.

Governor Yahaya Bello to President Yahaya Bello (GYB2PYB) support group ta aiko wa Legit.ng jawabinta, ta fito da nasarorin gwaninta, Yahaya Bello.

Ambasada Oladele John Nihi ya bayyana jawabin da aka ji ya fito daga kungiyar TSG ta bakin Kwamred Ibrahim a matsayin abin mamaki, kuma kage.

Kara karanta wannan

Kalaman Gwamnan Arewa kan zaben 2023 ya tsokano masa fada da Magoya-bayan Tinubu

Oladele John Nihi yake cewa an zo lokacin da matasa ke kokarin karbar mulki a fadin Afrika, ba Najeriya kadai ba, an daina yayin dattawa a kan mulki.

Legit.ng ta rahoto Ambasada Nihi yana cewa gwamnan ya na biyan albashi, sannan ya shigo da inshora da sauran tsare-tsare da ma’aikata ke cin moriya.

Takarar 2023: Cacar baki ta kaure tsakanin Magoya bayan Yahaya Bello da na Bola Tinubu
Yahaya Bello da Bola Tinubu Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Shawarar da GYB2PYB ta ba 'Yan Tinubu Support Group

“Za a iya yi wa Kwamred Ibrahim uzuri domin ya jahilci abubuwan da suke faru wa a kewayen jihar Kogi. Ya na ikirarin ma’aikata suna bin gwamna Yahaya Bello bashin albashi, hakan ya nuna bai dace ayi la’akari da su a neman shugaban kasa ba.”
“Ibrahim da Tinubu Support Group suna bukatar su daina wasa da bayanai, idan suna so su tallata Baba, wanda tsofai-tsofai ne shi ga matasan zamanin nan.”

Kara karanta wannan

Babu ruwanmu da ‘yarjejeniyar’ Buhari da Tinubu, 2023 lokacin matasa ne inji Yahaya Bello

Shugaban kungiyar ta GYB2PYB yace Amurka ta ayyana Kogi a matsayin inda ake zaman lafiya, ta na cikin inda aka fi ko ina kwanciyar hankali a Najeriya.

“Saboda haka muna kira ga darektan wannan kungiya ya yi cikakken binciken kafin ya fito yana neman cin mutuncin baban ‘dan siyasar da ake takama da shi.”

Babu abin da Bello ta tsinana a Kogi?

A jiya kun ji cewa magoya bayan Bola Tinubu sun sa kafar wando daya da Yahaya Bello a kan batun 2023, inda su kayi tir da harin shugabancin Najeriya da yake yi.

TSG ta ce afuwar mutanen Kogi ya kamata Yahaya Bello ya nema ba takarar shugaban kasa ba. Amma Magoya baya sun ce gwamnatinsa na shimfida ayyuka a Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel