Babu ruwanmu da ‘yarjejeniyar’ Buhari da Tinubu, 2023 lokacin matasa ne inji Yahaya Bello
- Yahaya Bello yace mutane da yawa suna rokonsa ya nemi shugaban kasa
- Gwamnan na Kogi ya ba Bola Tinubu shawarar ya hakura da mulki a 2023
- Bello ba ya tare da wata yarjejeniya da aka ce Buhari ya shiga da su Tinubu
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi hira da Daily Trust, inda ya yi magana a kan tafiyar APC, 2023, Bola Tinubu da kuma mulkin Muhammadu Buhari.
Yahaya Bello zai yi takara a 2023?
Yahaya Bello ya bayyana cewa daga masu tallar tumaturi a hanya, zuwa masu bara da kanikawa, suna ta rokon shi ya fito takarar shugaban kasa a 2023.
Gwamnan yace ba zai ba su kunya ba, ya nuna da shi za a shiga neman mulkin kasar nan a 2023.
Bola Tinubu ya hakura - Bello
"Sanata Tinubu yana cikin jagororinmu, ina ganin girmansa, ya taimaki siyasar Najeriya, ya shuka yara da yawa, shawara ta shi ne ya bar yara su yi mulki."
“Ya kyale yaran da ya rena su yi shugabanci, ya ga gudun ruwansu, ya ga yadda za mu mulki kasar nan a zamaninsa. Amma yana da damar da zai fito takara.”
Tinubu zai iya sauya-sheka?
Bello yana ganin cewa tsohon gwamnan na jihar Legas, Bola Tinubu ba zai balle daga jam’iyyar APC da ya gina, saboda bai samu yadda yake so a zaben 2023 ba.
“Ba za ka gina gida, sannan ka dawo ka ruguza shi ba. A matsayinsa na dattijo, ba zai yi haka ba.”
A game da abin da Sanata Rufai Hanga ya fada na cewa akwai tsohuwar yarjejeniya tsakanin Muhammadu Buhari da Bola Tinubu, gwamnan yace babu ruwansu.
“Jam’iyyar APC tana aiki ne da kundin tsarin mulki wanda kowa ya karanta, ya fahimta. Najeriya kasa ce mai tsari, ba mallakin wani mutum daya ko biyu ba ne.
“Ba na nan lokacin da aka yi wannan magana. Yau muna da mabiya mutum miliyan 40 a APC, ba da mu aka yi ba, sai ka ce mana dole mu bi wancan yarjejeniya?”
Bello yace Buhari da Tinubu suna neman ‘dan takara mai farin-jini ne a zabe, amma babu maganar shigo da tsarin siyasar ‘daga kai sai abokanka’ a zamanin yau.
Gumi ya yi zazzaga
An ji cewa malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki Malaman addini da shugabannin siyasa, yace malamai sun koma ‘Yan amshin shatan masu mulki a Najeriya.
Ahmad Gumi ya yi Allah-wadai kan yadda yan siyasa suka yi amfani da dukiyar al'umma wajen baja koli da hayar jiragen sama zuwa bikin Yusuf Buhari da Zahra Bayero.
Asali: Legit.ng