2023: Masu zuwa biki a Bichi sun ci karo da fastocin Gwamna Ganduje da Yemi Osinbajo

2023: Masu zuwa biki a Bichi sun ci karo da fastocin Gwamna Ganduje da Yemi Osinbajo

  • Mutane sun wayi gari da fastocin Dr. Abdullahi Ganduje da Yemi Osinbajo a Kano
  • Wadanda suka halarci bukukuwan da aka yi a garin Bichi sun ci karo da hotunan
  • Wata kungiya tana so Farfesa Osinbajo da Gwamnan jihar Kano suyi takara a 2023

Kano - Fastocin yakin neman zaben shugaban kasa a 2023 masu dauke da hotunan Abdulahi Umar Ganduje da Yemi Osinbajo sun fara yawo a jihar Kano.

Hadin Abdullahi Umar Ganduje da Yemi Osinbajo

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa wadannan fastoci da aka fitar samfuri-samfuri suna dauke da tambarori irinsu ‘Osinbajo-Ganduje Alliance (OGA)’.

A wasu fastocin kuma za a ga an rubuta ‘OGA Na Master’ ko kuma ‘For Better Nigeria’. Oga ya na nufin tarayyar Abdullahi Ganduje da mai girma Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Daurin auren Yusuf Buhari: Jiragen Alfarma fiye 25 ne suka dira a Kano, Ƴan Nigeria sunyi martani

Fastocin sun nuna mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo zai nemi kujerar shugaban Najeriya, yayin da gwamnan zai yi masa takarar mataimaki.

An ga hotunan Oga 2023 a hanyar Bichi

Magoya baya sun lika wadannan hotunan ne a manyan hanyoyin da aka san jama’a za su bi a garin Kano a lokacin da aka yi bikin ‘dan shugaban kasa a Bichi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karshen makon da ya gabata ne manyan mutane suka cikin garin Bichi domin halartar auren Yusuf Buhari da ‘diyar Sarkin Bichi, Zahra Nasiru Ao Bayero.

Gwamna Ganduje da Yemi Osinbajo
Fostar Oga 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoton yace an ga wadannan hotuna a irinsu hanyar Ahmadu Bello, Murtala Muhammad da shatale-talen Kano club da kuma irinsu titin Independence way.

Sannan an ga hotuunan a hanyar zuwa filin jirgin sama, wanda ta nan ake bi domin zuwa garin Bichi, inda aka yi daurin aure da bikin ba Sarkin Bichi sandar girma.

Kara karanta wannan

Siyasa a gefe: Hotunan Fani-Kayode yayin da ya shiga sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Buhari

Shugabannin wannan tafiya ta Oga 2023, Oluleke Mose da Bello Adamu Mohammed sun shaida wa manema labarai suna tare da Ganduje da Osinbajo a zaben 2023.

Masu fashin bakin siyasa suna ganin za a iya jarraba takarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Yemi Osinbajo idan tafiyarsa Bola Tinubu ba ta yiwu a APC ba.

Bikin Yusuf Buhari

A wajen bikin Yusuf Buhari da Zahra Bayero, an ji Femi Fani-Kayode ya dawo yana yabon Ministan sadarwa, Dr. Isa Pantami da manyan APC, ya kira su ‘Yanuwa’.

A baya, Fani-Kayode ya caccaki Isa Pantami, ya kira sa ‘Dan ta’adda’, ya kuma huro wa Ministan wuta a kan zarginsa da ake yi da furta wasu kalamai a shekarun baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel