Bayan ya gama zagin Pantami, Fani-Kayode ya kira Minista ‘Abokinsa’ a wurin auren Yusuf Buhari
- An ji Femi Fani-Kayode yana cewa Dr. Isa Ali Pantami ‘Amini’ ‘Danuwansa' ne
- Kwanakin baya, ‘Dan adawar ya yi wa Ministan sadarwan kaca-kaca a Facebook
- Tsohon Ministan ya hadu da ‘Yan siyasa a wajen auren su Yusuf Buhari a Bichi
Kano - Watanni uku da kiran Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani da ‘dan ta’adda, an ji Femi Fani-Kayode, yana cewa Isa Ali Pantami mutuminsa ne.
Jaridar Punch ta rahoto Femi Fani-Kayode ya na kiran Dr. Isa Ali Pantami da ‘Amini, ‘Danuwa.’
Tsohon Ministan ya bayyana wannan ne a wajen bikin auren ‘diyar Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero da kuma ‘dan shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
A baya, babu irin sunayen da Femi Fani-Kayode bai kira Isa Ali Pantami ba, sai ga shi an ga ‘dan adawar ya hau jirgi tun jiya domin halartar auren a jihar Kano.
Siyasa a gefe: Hotunan Fani-Kayode yayin da ya shiga sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Buhari
A shafinsa na Twitter, Fani-Kayode ya nuna hotunan da ya dauka a hanyar zuwa auren da gwamnoni da jiga-jigan APC, daga ciki har da Dr. Isa Ali Pantami.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Pantami da manyan APC sun zama ‘yanuwan FFK
“Na bi jirgin sama na je Kano tare da abokai da ‘yanuwa na, gwamna Bello Matawalle na Zamfara, Babagana Umar Zulum na Borno, Sanata Sani Ahmed Yarima, Sanata Ali Ndume, Ambasada Bashir Yuguda, Minista, Isa Pantami, Mallam Nuhu Ribadu da sauransu.”
FFK yake cewa sun zo Kano ne domin halartar auren Yusuf Buhari da Zahra (Nasir) Ado Bayero.
Tsohon Ministan harkokin jirgin saman ya bada labarin irin cikar da aka yi a wajen daurin auren, da yadda suka yi tafiyar cikin lafiya, suka dawo cikin koshin lafiya.
“Tafiyar ta yi dadi, mun gode wa Ubangiji da aka isa lafiya. Kano ta cika, ta tumbatsa, gari ya dauka da murna, an ga ala’ada da tarihi. Na yi farin ciki halartar bikin.”
Mutumin da aka sani da sukar gwamnatin Muhammadu Buhari, ya rubuta wa mabiyansa a shafin Facebook cewa za su cigaba da jin yadda ta kasance da shi a taron.
A shafin na sa na Facebook, a baya, Fani-Kayode ya yi wa Dr. Pantami wanda malamin addini ne kaca-kaca.
An shirya liyafa ta musamman
Jinin sarauta ne ya hadu da masu mulki a yayin da aka yi liyafar cin abincin dare na auren Yusuf Muhammadu Buhari da gimbiya kuma amaryarsa, Zahra Bayero.
An ji cewa a ranar Alhamis dinnan ne, wanda yayi daidai da jaji-birin daurin auren masoyan biyu ne aka yi kasaitacciyar liyafar cin abinci na sai wanda ya gani.
Asali: Legit.ng