Sunday Igboho ba zai dawo Najeriya ba sai bayan gwamnatin Buhari, Lauyansa

Sunday Igboho ba zai dawo Najeriya ba sai bayan gwamnatin Buhari, Lauyansa

  • Gwamnatin Najeriya na cigaba da kokarin dawo da Sunday Igboho Najeriya
  • Jami'an tsaro a Kotono sun damkeshi yayinda yake kokarin guduwa Jamus
  • Hukumar DSS ta alanta neman Igboho ruwa jallo bayan da ta kai hari gidansa

Daya daga cikin lauyoyin Sunday Igboho, mai rajin kafa kasar Oduduwa, Olusegun Falola, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya zama shugaban kama karya.

Ya kara da cewa zaman da Igboho ke yi a jamhuriyyar Benin alheri ne gare sa.

Lauyan yace Sunday Igboho bai zai dawo Najeriya ba har zai bayan karewar wa'adin mulkin shugaba Buhari.

Falola ya bayyana hakan a wata hira da gidan rediyo kuma TheNation ta ruwaito.

Igboho ya kwashe wata guda a kurkuku kasar Benin tun lokacin da aka damkeshi ranar 19 ga Yuli, 2021 a Kotonou.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sunday Igboho ba zai dawo Najeriya ba sai bayan gwamnatin Buhari, Lauyansa
Sunday Igboho ba zai dawo Najeriya ba sai bayan gwamnatin Buhari, Lauyansa Hoto: Collage
Asali: Facebook

An ci taran ministan shari'a Malami N50,000 akan Igboho

Wata Babbar Kotun Jihar Oyo da ke zama a Ibadan ta tsawaita umurnin da ta bayar na hana hukumar tsaro na farin kaya daga kame dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho.

Mai shari'a Ladiran Akintola, wanda ya bayar da umurnin a ranar 4 ga watan Agusta a zaman da aka ci gaba da yi a ranar Laraba ya kuma ba da umarnin Malami ya biya N50,000 kasancewarsa wanda ake kara na farko.

An ba da umarnin biyan kudin daga Malami ne saboda shigar da martaninsa kan karar da Igboho ya shigar a kan lokaci.

Yarbawa sun gargadi Obasanjo kan shiga fadan Sunday Igboho da gwamnatin Buhari

Wata kungiya mai suna Yoruba for One Nigeria Forum (YONF), ta nemi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya janye kansa daga rahoton da ke cewa yana lallabin Jamhuriyar Benin don kare Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho daga fuskantar hukunci.

Kungiyar a cikin wata sanarwa mai taken, 'Olusegun Obasanjo shine babban mai cin gajiyar Hadin kan Najeriya' wanda Seun Adebayo Lawal, shugabanta na kasa ya sanya wa hannu, ya ce kiran ya zama tilas duba da irin fa'idodin da tsohon shugaban kasa daga hadin kan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng