Bam ya tarwatsa yan Shi'a yayin Muzaharar Ashura, mutum 50 sun jikkata

Bam ya tarwatsa yan Shi'a yayin Muzaharar Ashura, mutum 50 sun jikkata

  • Wasu sun sanya Bam cikin yan Shi'a masu muzahara a Pakistan
  • Wannan ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum uku
  • An dade ana kaiwa ya Shi'a hari idan suna tarurrukansu a Pakistan

Pakistan - Akalla mutum uku sun rasa rayukansu yayinda mutum 50 suka jikkata yayinda Bam ya tashi a tsakiyar mabiya akidar Shi'a yayin Muzahara a birnin Pakistan, cewar hukumomi.

Aljazeera ta ruwaito wani babban jami'in gwamnatin birnin Bahawalnagar da cewa:

"Muna masu tabbatar da labarin cewa mutum uku sun mutu yayinda 50 suka jikkata a tashin Bam."

A shafukan ra'ayi da sada zumunta, an ga bidiyoyin mummunar tashin Bam din yayinda jama'a ke kokarin taimakon wadanda suka jikkata.

Wani jami'in dan sanda, Kashif Hussain, ya tabbatar da wannan abu ga AFP.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira birnin Yola don gaisuwar ta'aziyyar Ahmad Joda

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Har yanzu bamu san yadda abin yake ba amma muna cigaba tattara bayanai daga wajen."

Bam ya tarwatsa yan Shi'a yayin Muzaharar Ashura, mutum 50 sun jikkata
Bam ya tarwatsa yan Shi'a yayin Muzaharar Ashura Hoto Pakistan
Asali: Facebook

Muzaharar Ashura ta yan Shi'a ta rikide zuwa rikici a Sakkwato birnin Shehu

A Najeriya kuwa, rikici ya barke tsakanin 'yan uwa mabiya akidar Shi'a da jami'an hukumar yan sanda a cibiyar daular Usmaniyya yayin Muzaharar ranar Ashura da akayi ranar Alhamis.

BBC ta ruwaito yan Shi'an da cewa yan sanda ne suka bude musu wuta lokacin da suke muzaharar.

A cewarsu, sun kammala zagayensu kenan yan sanda suka biyosu a baya suka harba musu barkonon tsohuwa.

Sun kara da cewa wannan harbi yayi sanadiyyar mutuwan akalla mutum 15 yayinda da dama sun jikkata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel