Secondus: Abin da ya sa aka ga mun yi zuga, mun ziyarci tsohon Shugaban kasa Obasanjo

Secondus: Abin da ya sa aka ga mun yi zuga, mun ziyarci tsohon Shugaban kasa Obasanjo

  • Prince Uche Secondus ya bayyana makasudin zuwansa wurin Olusegun Obasanjo
  • Shugaban na PDP yace sun gana da Obasanjo ne domin halin da Najeriya ta ke ciki
  • Secondus sun nemi tsohon shugaban kasan su hadu, su je su ba Gwamnati shawara

OgunPremium Times ta kawo cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya bayyana makasudin zuwansu gidan Olusegun Obasanjo.

Prince Uche Secondus yace ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne domin su tattauna game da abubuwan da ke faruwa yanzu a Najeriya.

Shugaban na PDP ya shafe kimanin sa’a guda yana tare da Cif Olusegun Obasanjo a babban dakin karatunsa da ke garin Abeokuta, jihar Ogun a ranar Alhamis.

Bayan zaman na su da aka yi a bayan labule, Mista Uche Secondus ya yi magana da manema labarai.

Kara karanta wannan

Obasanjo bayan gana wa da PDP: Najeriya na iya tabarbarewa idan ba a kula ba

Jaridar ta ce a jawabinsa, Uche Secondus yace ya zo ganin Obasanjo ne a matsayinsa na dattijon da ake jin maganarsa, domin ya ba gwamnati mai-ci shawara.

“Na zo ne tare da ‘yan tawagata da shugabannin jam’iyyar PDP na jihar Ogun, domin mu tatsi wani abu daga tarin ilmin Baba a matsayinsa na Dattijo.”

Secondus da Tsohon Shugaban kasa Obasanjo
Obasanjo da 'Yan Majalisar Secondus Hoto: www.akelicious.net
Asali: UGC

“A ‘yan kwanakin nan abubuwa sun yi kamari, Baba mutum ne da Duniya ta san da zaman shi, ya na shawo kan matsalolin da ake fama da su a ko ina.”
“Asali ma na samu labari kasar da Baba (Obasanjo) ya kai ziyara karshe ita ce Afghanistan, duk da halin da kasar ta ke ciki, ya je, ya dawo da ransa.”
“Saboda haka, ni da ‘yan tawagata mu na murna, da godiya ga Allah. Mun tattauna a kan Najeriya. Batun kasa aka yi kafin a kai ga maganar komai.”

Kara karanta wannan

Neman mafita: Secondus ya dira gidan Obasanjo yayin da rikicin PDP ya tsananta

Secondus yace duk da cewa ‘dan PDP ne shi, siyasa ba za ta yiwu ba tare da an samu zaman lafiya a kasa ba.

“Mun san rashin tsaro, mummunan halin tattalin arziki, satar mutane da ake yi a fadin kasar nan, shiyasa muke neman manya suje, su ba gwamnati shawara.”

Magoya bayan Saraki sun fara shirin 2023

Rahotanni na zuwa mana cewa ‘Yan kungiyar SarakiIsComingDoorToDoor 2023 sun yi wa kananan manoma abin alheri yayin da ake cikin tsakiyar damina.

Kungiyar Saraki Is Coming Door To Door 2023 Organisation na so tsohon shugaban majalisat dattawan na Najeriya ya fito ya nemi shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng