Yadda Jam’iyyar APC za ta zarce a kan mulki bayan 2023 inji Shugaban Majalisar Dattawa

Yadda Jam’iyyar APC za ta zarce a kan mulki bayan 2023 inji Shugaban Majalisar Dattawa

  • Shugaban majalisar dattawa ya gana da wasu matasa ‘Yan jam’iyyar APC
  • Ahmad Ibrahim Lawan yace dole APC ta cika alkawuran da ta yi wa jama’a
  • Dr. Ahmad Lawan ya na ganin hakan ne zai sa APC ta zarce a mulki a 2023

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya yi magana game da zabe mai zuwa na 2023, har ya ba gwamnatinsu shawara.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya na fada wa jam’iyyarsu ta APC mai mulki dabarar lashe zaben da za ayi a shekarar 2023.

Da yake magana a ranar Alhamis, 19 ga watan Agusta, 2021, ‘dan majalisar yace dole ne jam’iyyar ta cika duk alkawuran da ta daukar wa ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Rikicin cikin gidan da ya ke damalmala Jam’iyyar APC ya kara cabewa

Me Ahmad Lawan ya fada wa matasan APC?

Ahmad Ibrahim Lawan ya bayyana haka ne a lokacin da ya hadu da wani kwamitin matasa da ke kokarin ganin ana tafiya da su a cikin sha’anin mulki.

Baya ga cika alkawuran da jam’iyyar ta yi kafin ta samu kuri’un mutanen kasar nan a zaben 2019, Ahmad Lawan yace wajibi ne a rika tafiya da matasa.

Shugaban majalisar dattawan kasar yace akwai bukatar APC mai mulki ta tabbatar cewa tana sa matasa wajen duk wani mataki da za a dauka a kasa.

Shugabannin Majalisar Tarayya
Shugaban kasa da Shugabannin Majalisa Hoto: todaynewsafrica.com
Asali: UGC

Dole a dama da masu jini a jiki - Lawan

Har ila yau, Lawan ya na ganin yana da kyau matasa su zama cikin tsare-tsaren da gwamnati ta kawo.

Ta haka ne Ahmad Lawan yake ganin jam’iyyar APC za ta cigaba da rike mulki a Najeriya bayan 2023, lokacin da wa’adin Muhammadu Buhari zai cika.

Kara karanta wannan

2023: Cancanta ya kamata a bi wajen zabar wanda zai zama Shugaban Najeriya, in ji Yahaya Bello

‘Dan siyasar ya bayyana wa matasan cewa akwai kokarin da APC ta ke yi na ganin ta ci moriyar nasarorin da ta samu na mulki da rinjaye a majalisun kasar.

Jigon na APC yana kokarin tabbatar da cewa APC ta yi abin da zai kara bunkasa siyasar farar hula.

Sabani a jam'iyyar daga gida

Kun ji cewa akwai rikicin cikin gidan da yake nema ya barko wa jam'iyyar APC. An samu wadanda suka kai shugabannin APC da AGF gaban Alkali.

Wadannan fusatattun 'yan jam'iyya sun ce babu inda doka ta ba Ministan shari'a dama ya nada Gwamna Mai Mala Buni a matsayin shugaban APC na riko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel