Kashe-kashen Jos: Abubuwa 4 da muke so gwamnati tayi ko mu dauki mataki - Dahiru Bauchi

Kashe-kashen Jos: Abubuwa 4 da muke so gwamnati tayi ko mu dauki mataki - Dahiru Bauchi

  • Dahiru Usman Bauchi yana so a hukunta wadanda suka kashe Bayin Allah a jihar Filato
  • Shehin malamin ya bukaci a biya iyalan wadanda suka rasu diyya, a kula da masu rauni
  • Malamin yace an dade ana wannan, yana so ayi alkawari hakan ba zai sake aukuwa ba

Bauchi - Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnati ta hukunta wadanda ke da hannu wajen kashe matafiya a Jos.

BBC Hausa ta yi hira da shehin malamin, inda ya bayyana cewa an kure masu hakuri wannan karo, ganin yadda aka dade ana kashe masu mutane a Najeriya.

“InnaliLahi wa inna ilaihi rajiun!"

“InnaliLahi wa inna ilaihi rajiun! “InnaliLahi wa inna ilaihi rajiun!! “InnaliLahi wa inna ilaihi rajiun!!!
“Mu wannan abu, an dade ana yi mana, ‘yanuwa da suke zuwa zikiri ake tsare wa, ana kashe wa. Ba za mu yafe ba, ba za mu bari ba, ba za mu yi shiru ba.”

Kara karanta wannan

Wannan ba shine farko ba: Izala ta yi martani kan kashe Musulmai da aka yi a Jos

“Za mu dauki dukkan matakai da za a dauka wadanda shari’a ta yadda da su. Mu na kiran musulmi, muna bada hakuri cewa ka da a dauki mataki a hannu.”
“Ayi hakuri, muna bin gwamnati har mu ga inda suka tsaya. Idan inda suka tsaya bai yi mana ba, sai mu yi namu.”

Dahiru Bauchi a Aso Villa
Shugaban kasa da Dahiru Bauchi Hoto: www.solacebase.com
Asali: UGC

Wani mataki Shehi yake so a dauka?

Shehin yace na farko a biya diyyar wadanda aka kashe ga iyalansu, na biyu a hukunta wadanda suka yi laifin, kuma a dauki dawainiyar wadanda aka ji wa rauni.

“Sannan a dauki alkawari irin wannan abu ya zo karshe kenan, an katse shi ba zai kara faru wa ba.”

Malamin ya fadawa BBC idan masu rike da mukamai ba za su iya kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba, su sauka daga kujerunsu, su bari wasu su karbi mulkin.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

“Amma hakika an kure mu, an kure mana bakin hakurinmu. Mun fada a lalama, mun fada a cikin zafi.”

Sunayen wadanda suka mutu a kisan gillar Jos

A baya kun ji cewa yayin dawowa daga taron addu'o'in shiga sabuwar shekara a Bauchi, an auka wa wasu musulamai wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, an kashe su.

Wadannan Bayin Allah ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, aka tare motocinsu a Jos. Mutane 25 suka mutu, wasu sun ji rauni, ba a san inda da-dama suka shiga ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel