Abubuwa 5 da za ka sani game da rayuwar Marigayi Sanata Mantu da COVID-19 tayi ajalinsa

Abubuwa 5 da za ka sani game da rayuwar Marigayi Sanata Mantu da COVID-19 tayi ajalinsa

Abuja - A ranar 17 ga watana Agustan 2021, aka wayi gari da labarin cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu, ya rasu.

An bada sanarwar za a yi wa Sanata Ibrahim Mantu sallah a gidansa da ke Apo, birnin Abuja.

Legit.ng Hausa ta tsakuro kadan daga cikin wannan dattijo, fitaccen ‘dan siyasa, kuma daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya.

1. Yaushe aka haifi Mantu?

An haifi Ibrahim Mantu a ranar 16 ga watan Fubrairu, 1947, a kauyen Chanso, a yankin Gindiri, karamar hukumar Mangu, jihar Filato.

Rahotanni sun ce Sanata Mantu ya rasu ya na da shekara 74 bayan ya yi jinyar COVID-19.

2. Ina Mantu ya yi karatu da aiki?

Marigayin ya shiga makarantar firamare daga 1955 zuwa 1961 a Gindiri a karamar hukumar Mangu, ya samu shaidar kammala firamare a shekarar 1961.

Kara karanta wannan

Na so diyata ta kammala karatunta kafin aure, Sarkin Bichi kan shirin auren diyarsa da Yusuf Buhari

Daga nan ya fara aiki a matsayin Kilaki a 1962 a ma’aikatar ayyuka na gwamnati a Jos.

Daga baya Mantu ya koma makarantar horas da malamai da ke Gindiri a 1964, ya kammala karatu, har ya samu takardar shaidar zama malami a 1967.

Marigayi Sanata Mantu
Sanata Ibrahim Mantu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ng News ta ce marigayin ya yi aiki da kamfanin sigarin nan, Nigerian Tobacco da ke Zariya a 1968, bayan ‘yan shekaru ya koma aiki a kamfanin UAC.

Kamar yadda shafinsa na yanar gizo ya nuna, Sanata Mantu ya karanci ilmin siyasa a jami’ar Amurka da ake kira Washington International University.

An karrama Mantu a jami’ar aikin gona ta Makurdi, jami’ar Jos, Madonna University, Okija da wata jami’a da ke birnin Port Novo, da ke kasar Benin.

3. Yadda Mantu ya fara siyasa

Kara karanta wannan

Dan majalisar wakilai mai ci a jam'iyyar PDP ya rigamu gidan gaskiya

Sanata Mantu ta shiga siyasa a jamhuriyya ta biyu a shekarar 1978, ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar NPN na tsohuwar jihar Filato a 1980.

A lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya bada dama a dawo siyasa, Mantu ya nemi takarar shugabancin jam’iyyar NRC a Filato, amma bai dace ba.

Mantu ne shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan da jam’iyyar NRC ta shiga a 1993, daga baya gwamnatin soja ta soke wannan zabe.

4. Zuwansa Majalisar Tarayya a 1999

A 1998 Mantu ya zama sakataren yada labarai na jam’iyyar UNCP na kasa. Kafin Janar Abdusalam Abubakar ya soke zabuka, ya lashe kujerar Sanata.

Daga baya ya shiga jam'iyyar PDP da aka kafa, ya sake samun nasarar zama Sanatan Filato ta tsakiya. Sanata Mantu ya zarce a kan wannan kujera zuwa 2007.

5. Marigayin ya rike wasu kujeru da mukamai?

A Agustan shekarar 2001, Mantu ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa na kasa. Marigayin ya rike shugaban Alhazai na kasa a 2005 da 2006.

Kara karanta wannan

Matar tsohon shugaban kasa, Hadiza Shagari ta mutu bayan fama da cutar korona

Kun ji cewa Mantu ya rasu ya na cikin ‘yan majalisar amintattu na jam’iyyar PDP. Sanata ya na cikin dattawan da suka ba Goodluck Jonathan gudumuwa.

A wani jawabi da ya fitar, shugaba Muhammadu Buhari ya nuna alhini kan mutuwar Ibrahim Mantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel