Za ayi shari'a a kotu domin a kara wa Shugaban kasa Buhari da Gwamnoni wa’adi na uku

Za ayi shari'a a kotu domin a kara wa Shugaban kasa Buhari da Gwamnoni wa’adi na uku

  • Hon. Charles Oko Enya ya je kotu, yana so ayi wa tsarin mulkin Najeriya garambawul
  • ‘Dan siyasar yace tsarin mulki ya fifita ‘Yan majalisa kan Gwamnoni da Shugaban kasa
  • Oko Enya yana rokon a ba Shugaban kasa da Gwamnoni damar suyi wa’adi uku a ofis

Ebonyi - Rahotanni daga Aminiya sun tabbatar da cewa an shigar da kara a kotun tarayya da nufin ayi wa wa’adin masu mulki 'yar kwaskwarima.

Me doka ta ce a kan wa'adin masu mulki?

Daya daga cikin manyan APC, Charles Oko Enya, ya shigar da kara a kotu, yana so a ba gwamnoni da kuma shugaban kasa damar yin wa’adi uku a ofis.

Jaridar ta rahoto cewa Hon. Oko Enya, ya kai karar majalisar tarayya da ministan shari’a na kasa, a babban kotun tarayya da ke Abakaliki, jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

‘Dan siyasar yana so kotu ta yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima ta yadda za a cire takunkumin da aka sa wa masu mulki na yin wa’adi biyu.

A cewar Oko Enya, babu adalci idan ‘yan majalisa za su iya takara har sai sun gaji, amma shugaban kasa da gwamnonin ba su iya wuce shekara takwas.

Oko Enya ya dauko hayar Agboti Iheanacho

Barista Agboti Iheanacho shi ne babban lauyan da zai tsaya wa jigon na jam’iyyar APC a gaban Alkali.

Shugaban kasa Buhari
Shugaban kasa Buhari Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Takardun da aka gani a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, 2021, sun nuna Lauyan yana cewa sashe na 137(1)(b) ya takaita burin gwamnoni da shugaban kasa.

Agboti Iheanacho yake cewa wannan sashe da ya kayyade wa’adi biyu na shekaru hudu bai da hurumin zama a tsarin mulkin kasa saboda ba ayi adalci ba.

Kara karanta wannan

Dalilinmu na daina daukar sababbin ma’aikata a aiki a Gwamnati inji Ministan kwadago

Iheanacho ya roki kotu ta umarci Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, ya yi wa sashe na 127 na kundin tsarin mulkin kasar garambawul.

Jaridar ta ce Alkali zai saurari karar Charles Enya wanda ya yi wa jam’iyyar APC shugaban yakin neman zabe a jihar Ebonyi a zaben 2019 nan da makonni biyu.

Zaben shugabannin APC

Kungiyar Concerned Citizens of Like Minds, wanda ake kira CCLM ta bayyana ‘Dan takarar da ta ke goyon baya zaben kujerar shugaban Jam’iyyar APC na kasa.

Concerned Citizens of Like Minds tace Abdulaziz Yari ya fi kowa dace wa da ya zama shugaban APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel