Nasarawa Poly ta sallami dalibai 51 kan laifin satar amsa a Jarabawa

Nasarawa Poly ta sallami dalibai 51 kan laifin satar amsa a Jarabawa

  • An sallami akalla dalibai 51 daga makaranta kan laifin sata a jarabawa
  • Shugaban makarantar ya yi kira ga dalibai su yi watsi da satar amsa a jarabawa
  • Wannan ya biyo bayan sallamar dalibai biyu da aka kan shiga kungiyar yan daba

Nasarawa - Hukumar makarantar fasaha ta jihar Nasarawa watau Naspoly ta fittitiki dalibar 51 kan laifin satar amsa a jarabawar da aka gudanar a kakar karatun 2019/2020.

Mai magana da yawun makarantar, Uba Maina, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba, rahoton NAN.

Mana yace kwamitin ingancin ilimi na makarantar ta amince da a sallami daliban.

Ya lissafa daliban tsangaya-tsangaya da aka sallama, daga cikinsu har da dalibai aikin jarida.

Yace:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

"An sallami daliban ne kan laifuka daban-daban da ya shafi jarabawa. Cikinsu akwai masu zaune a makaranta kuma akwai yan jeka-ka dawo."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Daliban da aka sallama na karatun karamin Difloma ne ND da babban Difloma HND a tsangayar Injiniyanci, Akawun, aikin jarida, dss."

Nasarawa Poly ta sallami dalibai 51 kan laifin satar amsa a Jarabawa
Nasarawa Poly ta sallami dalibai 51 kan laifin satar amsa a Jarabawa
Asali: UGC

Maina ya kara da cewa shugaban makarantar, Abdullahi Ahmed, ya umurci daliban da aka kora sun mika dukkan dukiyar makaranta dake hannunsu wa shugabannin tsangayarsu.

Ya yi kira ga dalibai su yi watsi da satar amsa a jarabawa kuma su daina bin abokan banza don cigaban makarantar.

An Cafke Wani Dalibin Jami'a Ya Yi Shigar Mata Ya Zauna Jarabawar Budurwarsa

A wani labarin kuwa, wani ɗalibin ƙasar Senagal ya shiga hannu bisa zargin ya yi shigar mata kuma ya zauna wa budurwarsa jarabawa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

Lauyan dalibin ne ya bayyana haka kuma yace ita ma budurwar tasa ta shiga hannun dukkan su a zarginsu da aikata zamba cikin aminci.

A halin yanzun saurayi da budurwar tasa an gurfanar da su a gaban kotu a kan karar aikata zamba da kuma haɗa kai don aikata zamba cikin aminci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng