DHQ: Shugabannin Kungiyar ISWAP sun gigice, ganin Boko Haram suna ta ajiye kayan yaki

DHQ: Shugabannin Kungiyar ISWAP sun gigice, ganin Boko Haram suna ta ajiye kayan yaki

  • Rundunar sojin Najeriya tace nasarorin da ake samu yana birkita jagororin ISWAP
  • Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar da jawabi na musamman daga DHQ
  • Onyema Nwachukwu yace mayakan Boko Haram na ta cigaba da ajiye kayan fada

Rundunar sojojin kasa na Najeriya tace ‘yan ta’addan Islamic State of West Africa Province (ISWAP) watau Boko Haram sun shiga rudani a halin yanzu.

Darektan hulda da jama’a na sojin kasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana haka a jawabin da ya fitar a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, 2021.

Daily Trust ta rahoto Janar Onyema Nwachukwu yana cewa manyan shugabannin Islamic State of West Africa Province suna cikin wani yanayi na dar-dar.

A jawabinsa, Janar Onyema Nwachukwu yace ‘yan ta’addan sun koma amfani da furofaganda a wasu tashoshi domin yi wa mutanen Arewa maso gabas burga.

Kara karanta wannan

Yadda mu ka ga bayan ‘Yan bindiga 123 a ‘Jihar Zamfara a cikin ‘yan kwanaki Inji Dakarun Soji

Amir Manye Aga da mutanensa sun tuba

Babban jami’in gidan sojan yake cewa jagororin ISWAP sun kara birkice wa ne yayin da suka ga mayakansu sun sallama kansu da iyalansu a garin Mafa, Borno.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nwachukwu yace ‘yan ta’addan Boko Haram 186 a karkashin jagorancin shugabansu, Manye Aga, suka kai kansu gaban dakarun Operation HADIN KAI a Ajiri.

Janar Lucky Irabor
Shugaban Sojoji na kasa, Janar Lucky Irabor
Asali: Facebook

Tawagar Amir Manye Aga ta na kunshe da manyan maza 67, manyan mata 54 da kananan yara 65.

Sojoji sun karbe manyan makamai a hannun ‘yan ta’addan Boko Haram da suka tuba. Sanarwar ta ce an samu bindigogin AK-47 da harsashi a hannun mayakan.

Har ila yau, Janar din yace sojoji na tsare da wasu 'Yan Boko Haram daga kauyukan Landanli, Azah, Ngaridua da Kondilla, da suka sallama kansu a garin Bama.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto jami’in yana cewa sojoji zasu cigaba da amfani da sauran hanyoyi wajen ganin kawo karshen ta’addanci a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Hatsabibin Mayakin Boko Haram da Sojoji suka ce sun kashe a 2019, ya mika kansa da kansa

Ayi hattara da tubabbun Boko Haram - Ndume

Sanata Ali Ndume ya ja-kunnen jami'an tsaro a kan shagwaba tsofaffin ‘Yan Boko Haram, yace a ji da mutanen da aka yi wa ta’adi kafin a karbi tuban ‘Yan Boko Haram.

Ali Ndume ya jinjina wa irin kokarin da dakarun sojojin kasa ke yi yanzu. Sanatan yace dama ya san rashin kayan aiki ne ya hana Sojojin Najeriya kokari sosai a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel