Sojin saman Najeriya sun sheke shugabannin 'yan bindiga 3 a dajin Kuyambana dake Zamfara

Sojin saman Najeriya sun sheke shugabannin 'yan bindiga 3 a dajin Kuyambana dake Zamfara

  • Zakakuran sojin saman Najeriya sun yi nasarar halaka jiga-jigan shugabannin 'yan bindiga 3 a dajin Kuyambana da wasu miyagun
  • A karkashin ayyukan Operation Hadarin Daji, sojin sun sheke Habu Nabayye, Isuhu Sadi da Murtala Danmaje
  • Mazauna yankin a Zamfara sun bayyana jin dadinsu tare da godiyarsu inda suka ce hakan zai inganta tsaron yankin

Zamfara - Dakarun sojin saman Najeriya sun yi nasarar sheke shugabannin 'yan bindiga 3 tare da wasu miyagu a dajin Kuyambana dake jihar Zamfara.

Cigaban ruwan wutan da ake yi wa miyagun 'yan bindigan ya janyo ajalin shugabannin 'yan bindigan da suke ta'addaci a jihar Zamfara, PRNigeria ta ruwaito.

Sojin saman Najeriya sun sheke shugabannin 'yan bindiga 3 a dajin Kuyambana dake Zamfara
Sojin saman Najeriya sun sheke shugabannin 'yan bindiga 3 a dajin Kuyambana dake Zamfara. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kamar yadda wani jami'in sirri da aka yi ragargaza ta jiragen yakin tare da shi ya sanar, yace an sheke shugabannin 'yan bindigan a dajin Kuyambana, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Shugaban Jam'iyyar APC da Aka Sace

Majiyar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabannin 'yan bindigan na cigaba da addabar jama'a da basu ji ba, basu gani ba a jihar Zamfara. Sojin saman sun sheke a kalla miyagu arba'in da biyar karkashin ayyukan Operation Hadarin Daji.
Shugabannin 'yan bindigan da aka sheke yayin samamen sun hada da Habu Nabayye, Isuhu Sadi da Murtala Danmaje.
Wasu mazauna yankin sun bayyana godiyarsu kan wannan samamen da aka kaiwa 'yan ta'addan inda suka ce za a kara samun ingancin tsaro a yankin.

Gwamna Zulum ya gana da Janar Irabor kan tubabbun 'yan Boko Haram

A matsayin hanyar bullo wa tubabbun ‘yan Boko Haram daga bangarori daban-daban na jihar Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kai ziyara Abuja wurin shugaban sojin kasa, Janar Lucky Irabor a ranar Litinin.

Za a yi taron sirrin ne don Zulum ya nemi sanin dabaru na shawo kan rashin tsaro a jihar Borno kuma masu fadi aji sune suka taso da batun samar da shirin ‘Operation Safe Corridor’ don tabbatar da jin dadi da walwala saboda karya guiwoyin sauran ‘yan ta’addan da basu tuba ba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Kansila da Jaririnta Dan Wata 7 a Zamfara

Idan ba a manta ba, A ranar Asabar Zulum ta kai ziyara Bama da Gwoza don tattaunawa da shugabannin sojojin yankin da shugabannin garuruwan, prnigeria ta ruwaito.

Anan ne ya bayyana shirin sa na z ama da shugaba Muhammadu Buhari, shugaban hukumar sojin kasa, sauran shugabannin tsaro, shugabannin addinai, manyan kasa, malaman addinai na kasa da jihohi da sauran manya wadanda suka fuskanci matsalolin rashin tsaro don lamarin ya tsananta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng