Mata sun kai korafi kan yadda mazajensu ke takara da jariransu wajen shan mama

Mata sun kai korafi kan yadda mazajensu ke takara da jariransu wajen shan mama

  • Gwamnatin kasar Tanzania ta gargadi maza su daina takara da jarirai wajen shan mama
  • Gwamnatin tace wannan abu da maza ke yi na hana jariran shan isasshen ruwan mama
  • Wannan ya biyo bayan shawaran da aka ba maza su rika shan ruwan mama saboda yana kara karfin maza

Tanzania - Gwamnatin kasar Tanzania ya yi kira da babban murya ga wasu mazaje dake takaran nono da 'yayansu cewa su daina saboda hakan na hana jariran samun isasshen abinci.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan murnar ranar shayar da yara mama da akayi ranar 7 ga Agusta.

Gwamnati tayi wannan gargadi ne ga maza bayan wasu mata sun yi korafi cewa mazajensu na shanye nonon kuma 'yayansu sun daina samun isasshen ruwan nono.

A bidiyon da Millard Ayo TV ta daura, an ga Kwamishanan yankin Handeni, Siriel Shaidi Mchembe, tana cewa mazan sun fara wannan abu ne kan labarin da suka samu cewa ruwan mama na kara karfin maza.

Tace:

"Mun yanke shawaran bayani da babban murya cewa mazaje su daina shan nonon jarirai."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mata sun kai korafi kan yadda mazajensu ke takara da jariransu wajen shan mama
Mata sun kai korafi kan yadda mazajensu ke takara da jariransu wajen shan mama
Asali: UGC

Masana kiwon lafiya sunce mata su rika baiwa mazajensu na aure mama suna sha

Wata Masaniya kiwon lafiya kuma babbar Malamar jinya a jihar Legas, Mrs Rseline Oladimeji, a ranar Alhamis ta shawarci mata masu juna biyu su bari mazajensu suna sha musu mama.

A cewarta, wannan na da muhimmanci sosai domin shiryawa shayar da jariran da zasu haifa.

Oladimeji ta bada wannan shawara ne a wani shirin wayar da kan mata da aka yi don murnar zagayowar ranar shayarwa ta duniya, rahoton NAN.

Tace:

"Ku bar mazajenku su sha nononku yayinda kuke da ciki. Bayan dankon soyayya da hakan ke karawa, zai taimakawa kan nonon fitowa don shayar da jaririnku."

Asali: Legit.ng

Online view pixel