Ku rika baiwa mazajenku na aure mama suna sha, Masana kiwon lafiya ga mata

Ku rika baiwa mazajenku na aure mama suna sha, Masana kiwon lafiya ga mata

  • An yi kira ga mata su rika kula da mazajensu kamar jarirai
  • Masana sunce shan mama na kara dankon auratayya kuma yana taimakawa matan
  • Musamman masu juna biyu, zai saukake musu shayarwa bayan sun haihu

Wata Masaniya kiwon lafiya kuma babbar Malamar jinya a jihar Legas, Mrs Rseline Oladimeji, a ranar Alhamis ta shawarci mata masu juna biyu su bari mazajensu suna sha musu mama.

A cewarta, wannan na da muhimmanci sosai domin shiryawa shayar da jariran da zasu haifa.

Oladimeji ta bada wannan shawara ne a wani shirin wayar da kan mata da aka yi don murnar zagayowar ranar shayarwa ta duniya, rahoton NAN.

Tace:

"Ku bar mazajenku su sha nononku yayinda kuke da ciki. Bayan dankon soyayya da hakan ke karawa, zai taimakawa kan nonon fitowa don shayar da jaririnku."
"Hakazalika zaku iya shafa man Vaseline a dare kafin barci. Hakan na taimakawa wajen tausasa kan nono."

Kara karanta wannan

Sokoto da sauran jihohin Najeriya guda 5, da yadda sunayensu suka samo asali

Ta yi kira ga mata su shiryawa shayarwa domin gujewa matsalar rashin ruwan nono bayan haihuwa.

Ta kara da cewa sinadarin 'Colostrum' , wani ruwa mai kalan ruwan kwai dake fitowa bayan haihuwa na dauke da wasu sunadarai masu kara karfin garkuwan jikin jariri.

"Shima abin ruwan nono ne," tace.

Oladimeji ta gargadi mata kan cin wasu nau'ikan abinci da magunguna da ka iya cutar da jariransu idan suka fara shayarwa.

Ta bayyana cewa shan giya domin kara ruwan nono na da illa saboda yaron zai rika shan giyan daga nonon.

Ku rika baiwa mazajenku na aure mama suna sha, Masana kiwon lafiya ga masu ciki
Ku rika baiwa mazajenku na aure mama suna sha, Masana kiwon lafiya ga mata
Asali: UGC

KU RIKA CIN ABINCI MAI LAFIYA

Wata masaniyar nau'ikan abinci, Ms Gbemisola Ogungipe, ta shawarci iyaye masu shayarwa su rika cin abinci mai lafiya kuma su rika shan ruwa sosai.

Tace:

"Mace mai shayarwa ta rika cin nama, kifi, kwai da ganye a abincinta. Hakazalika ta rika shan lemu da kayan itace."
"Ta rika shan abubuwan ruwa irinsu madara, yoghurt, ice cream da koko."

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel