Gwamnatin tarayya zata ci bashin N4.89trn don daukar nauyin kasafin 2022

Gwamnatin tarayya zata ci bashin N4.89trn don daukar nauyin kasafin 2022

  • Gwamnatin tarayya tana neman bashin cikin gida da waje na naira tiriliyan 4.89 don cikasa kasafin kudin shekarar 2022 na naira tiriliyan 5.62
  • Ministar ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed ce ta gabatar da wannan kudirin ga ‘yan majalisar wakilai a ranar Litinin
  • A cewarta bisa tsarin kasafin shekara mai zuwa, gwamnatin tarayya zata rage yawan kudaden da take narka wa ma’aikatu, sasanni da hukumomi da naira biliyan 259.31

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirinta na amso rancen cikin gida da na waje na naira tiriliyan 4.89 don samar da kudaden kasafin shekarar 2022 na naira tiriliyan 5.62.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Ministar kudi ta bayyana wannan kudirin a wata takarda da ta mika ga ma’aikatarta ne ga majalisar wakilai ta MTEF da FSP na 2022 zuwa 2024 a ranar Litinin.

Gwamnatin tarayya zata ci bashin N4.89trn don daukar nauyin kasafin 2022
Gwamnatin tarayya zata ci bashin N4.89trn don daukar nauyin kasafin 2022. Hoto daga Zainab Shamsuna Ahmed
Asali: Facebook

Ministar ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, a gabatarwar da tayi ta ce gwamnatin tarayya za ta rage yawan kudaden da take narkawa ma’aikatu, sasanni da hukumomi da naira biliyan 259.31.

Ta bayyana yadda gibin da za a isa dashi 2022 na naira tiriliyan 5.62 ya karu fiye da naira tiriliyan 5.60 a 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Za a yi amfani da kudin da za a ranta daga ciki da wajen kasar nan na naira tiriliyan 4.89 wurin cikasa gibin da aka samu.

'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi awon gaba da kayan abinci a Abuja

Masu garkuwa da mutane sun harbe wanimatashi, Haruna Dako, sannan sun sace kayan abinci iri-iri a Kambu dake wuraren Abaji a birnin tarayya, Abuja.

Daily Trust ta ruwaito yadda kauyen Kambu, wanda yake karkashin Chakumi yakeda iyaka da Gwagwalada, inda Rafin Gurara yake gudana tsakanin garuruwan.

Mazaunin garin mai suna Yahaya ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 10:27 na dare lokacin da masu garkuwa da mutane suka shigo garin da yawansu.

Marigayin ya fito daga gidansa ne ya kai cajin wayarsa wani shago, kwatsam masu garkuwa da mutanen suka tsare shi.

Ya je bayar da wayarsa caji ne a wani shago yana hanyar komawa gida ya gamu da daya daga cikin ‘yan bindigan wanda ya umarce shi da ya tsaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel