IBB, Obasanjo, Saraki, da jiga-jigan PDP sun yi ganawar sirri
- Tsohon shugaban kasan mulkin Soja na murnar cika shekaru 80 a duniya
- Manyan yan siyasa sun ziyarcesa a fadar dake Minna, jihar Neja
- Jiga-jigan APC sun yi amfani da damar wajen tattauna lamarin siyasa
Minna - Jiga-jigan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Talata sun yi ganawar sirri a gidan tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, dake Minna, jihar Neja.
Ganawar Minna wacce akayi ranar cikar IBB shekaru 80 ta samu hallarar Janar Ibrahim Babangida; tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo; da tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.
Sauran sune shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus; gwamnan jihar Akwa Ibom, emmanuel Udom; tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi; Sanata Philip Aduda, Ben Ibo da sauran jiga-jigan jam'iyyar.
An yi wannan zama ne yayinda ake shirin zaman majalisar zartaswar PDP ranar Alhamis yayinda ake shirin taron gangami a watan Oktoba.
A cewar majiya, anyi ganawar ne don shirya yadda abubuwa zasu kasance a taron gangamin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dirar Obasanjo Minna ke da wuya, sauran jiga-jigan suka shiga ganawar sirri saboda an hana yan jarida shiga.
Daga cikin wadanda suka shiga tare da Obasanjo sune Janar Aliyu Gusau (mai ritaya) da Janar Aliyu Akilu (mai ritaya).
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa sabanin murnar cikar Babangida shekaru 80, dattawan sun yi amfani da daman wajen tattauna abubuwan dake faruwa a kasar.
Wata majiya a cikin ganawar da ta bukaci a sakaye sunanta tace:
"Ba haka kawai aka hana ku (yan jarida) shiga cikin gidan ba. Sun san abinda suke yi, yan jarida ka iya hanasu tattaunawa yadda suke so."
"Kamar yadda kuke gani, ba yan jarida kadai ba; har wasu makusantan IBB ba'a bari sun shiga ba. Wannan murnar ranar haihuwar ta baiwa manyan mutanen damar tattaunawa."
Ba za'a tsige Uche Secondus daga jagorancin PDP ba, Shugabannin jam'iyya
Jam'iyyar PDP ta ce ba za'a tsige Prince Uche Secondus daga kujerarsa ba amma za'a gaggauta gudanar da taron gangami a Oktoba.
Asali an shirya gudanar da taron gangamin ne a Disamba, karshen shekara.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP ne yayi sanarwar ranar Talata bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki suka gudanar a Abuja.
Asali: Legit.ng