Kyawawan Hotuna da bidiyon kafin aure na Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero
- Zuka-zukan hotuna tare da bidiyon kafin aure na Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero suna fara bayyana
- Wurin daukan hoto mai suna @wraith_studios ne suka wallafa kyawawan hotunan ango da amaryar da suka yi shigar al'ada
- Ko shakka babu, idan mai kallo ya duba hotunan da bidiyon, za a gane cewa auren soyayya ne sakamakon shaukin kauna dake diban masoyan
Kano - Kyawawan hotunan kafin aure na Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero sun fara bayyana a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.
Ana ta shirin bikin da daya namiji tilo na gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gimbiya Zahra, diya ga sarkin Bichi a jihar Kano.
Kamar yadda hotuna tare da bidiyo da suka fara bayyana na kafin bikin suka nuna, babu shakka auren soyayya ne za a kulla tsakanin diyar basaraken da dan shugaban kasan.
A daren Talata ne wurin daukar hoto mai suna @wraith_studios dake Abuja suka wallafa kyawawan hotunan kyakyawar amarya Zahra tare da angonta.
A hotunan da suka bayyana, an ga ango tare da amaryar sanye da kayan gargajiya yayin da suke cike da shaukin soyayya da kaunar juna.
Babu shakka an yi hotunan ne cike da nuna salon al'adu saboda an ga ango Yusuf sanye da kayan sarauta tare da nadi inda amarya Gimbiya Zahra Bayero ta bayyana da kayan saki.
Wadannan kyawawan hotunan kuwa sun sha Allah sam barka daga bakin jama'a domin kuwa an ga tsabar al'ada ta Malam Bahaushe da aka nuna a tattare dasu.
Za a daura auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero ne a ranar Juma'a mai zuwa a fadar Sarkin Bichi, Mai Martaba Alhaji Nasir Ado Bayero a Bichi dake jihar Kano.
Tun a makon da ya gabata ne aka fara shagulgulan bikin gidan shugaban kasan da na sarauta inda aka fara da wasan polo kafin wankan amarya ya biyo baya.
Nasara daga Allah: Sojoji sun cafke hadimin gwamna dake daukar nauyin 'Unknown Gunmen' a Kudu
Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar damko hadimin gwamna ne wanda yake kulle-kullen rura wutar ta’addanci a kudu maso gabas.
An bankado wanda ake zargin yana da hannu akan kaiwa mutanen gari da jami’an tsaro farmaki a kudu maso gabacin Najeriya.
PRNigeria ta tattaro bayanai akan yadda wani Tochukwu Okeke alias Owo, hadimin gwamna a kudu maso gabas ya daurewa ‘yan bindiga gindi kamar yadda rundunar division 82 na sojin Najeriya a Enugu suka bankado.
Asali: Legit.ng