Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya, Messi ne na daya

Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya, Messi ne na daya

  • Duk da komawa PSG, Lionel Messi ne dan kwallo mafi yawan albashi a duniya
  • Dan kwallon wanda ya koma kasar Faransa taka leda zai rika kwasan £960,000 a kowani mako (N546m)
  • Cristiano Ronaldo da Neymar ne suka zo na biyu da na uku

Bayan komawar Lionel Messi taka leda a kungiyar kwallon Paris Saint-Germain, zai rika amsan N546m a mako kuma shine dan kwallo mafi yawan albashi a duniya.

GiveMeSport ta lissafo manyan yan kwallon duniya 10 da suka fi daukan albashi.

Dan wasan kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo na daukan £900,000 yayinda Neymar na kungiyar PSG na daukan £606,000.

Ga jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya, a cewar The Radio Times:

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta ce a karbe N241m da aka karkakatar daga ofishin Hadimin Shugaba Buhari

10. Robert Lewandowski – £350,000-a-mako(kimanin N200million)

9. David De Gea – £375,000-a-mako(kimanin N214million)

8. Kevin De Bruyne – £385,000-a-mako (kimanin N219million)

7. Kylian Mbappe – £410,000-a-mako (kimanin N233million)

6. Gareth Bale – £500,000-a-mako (kimanin N285million)

5. Luis Suarez – £575,000-a-mako (kimanin N327million)

4. Antoine Griezmann – £575,000-a-mako (kimanin N327million)

3. Neymar – £606,000-a-mako (kimanin N345million)

2. Cristiano Ronaldo – £900,000--a-mako (kimanin N512million)

1. Lionel Messi – £960,000--a-mako (kimanin N546million)

Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya, Messi ne na daya
Jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya, Messi ne na daya
Asali: Getty Images

Jerin ‘yan wasan kwallon kafan da ba a taba yin irinsu ba a duniya

A bangare guda, an fito da jerin ‘yan wasan kwallon kafan da ba a taba yin irinsu ba. France Football ce tayi wannan aiki da taimakon wasu kwararrun ‘yan jarida 140.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kara kudin lambar mota da lasisin tuki da 50%, kalli jerin karin da akayi

Jaridar The Sun ta ce an zabi rukunin ‘yan wasa 11 har kashi uku. Irinsu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suna cikin sahun farko na jerin taurarin.

Rahoton ya tabbatar da cewa tsofaffin ‘yan wasa Pele da marigayi Diego Maradona sun samu shiga wannan sahu, amma babu wurin Zinedine Zidane.

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel