Gwamnati ta kara kudin lambar mota da lasisin tuki da 50%, kalli jerin karin da akayi

Gwamnati ta kara kudin lambar mota da lasisin tuki da 50%, kalli jerin karin da akayi

Kaduna - Wani rahoton ThePunch ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da karin kudin lambar mota da kuma lasisin tuki a fadin Najeriya.

Rahoton ya nuna cewa hukumar haraji JTB ta yanke shawaran ne a ganawarta ta 147 da akayi a Kaduna ranar Alhamis, 25 ga Maris.

Legit.ng ta tattaro cewa JTB ta aika wasikar aiwatar da umurnin ranar Juma'a, 30 ga Yuli ga dukkan hukumomi a jihohi da tarayya.

A cewar wasikar, shugaban JTB yace a fara aiwatar da sabon farashin ranar 1 ga agusta.

Shugaban hukumar haraji ta kasa FIRS ke jagorancin JTB.

Gwamnati ta kara kudin lambar mota da lasisi tuki da 50%, kalli jerin karin da akayi
Gwamnati ta kara kudin lambar mota da lasisi tuki da 50%, kalli jerin karin da akayi Photo credits: STEFAN HEUNIS/AFP, Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

Kara karanta wannan

Kungiya ta rubutawa Gwamnoni, ‘Yan Majalisa takarda, tace Osinbajo ya dace ya gaji Buhari

Ga jerin sabbin farashin da aka sa:

Lambar Mota:

Standard private and commercial number plates

Motocin haya da marasa haya - (Sabon farashi: N18,750; Tsohon farashi: N12,500)

Lambar mota na gayu - (Sabon farashi: N200,000; Tsohon farashi: N80,000)

Lambar babur - (Sabon farashi: N5,000; Tsohon farashi: N300)

Lamba na musamman - (guda uku) - (Sabon farashi: N30,000; Tsohon farashi: N2,000)

Lambar mota na daban - (Sabon farashi: N50,000; Tsohon farashi: N40, 000)

Lambar motar gwamnati - (Sabon farashi: N20,000; Tsohon farashi: N15,000)

Lasisin Tuki

Lasisin mota (shekara uku) - (Sabon farashi: N10,750; Tsohon farashi: N60,000)

Lasisin motta (Shekara biyar) - (Sabon farashi: N15,000; Tsohon farashi: N10,000)

Lasisin Babur/Keke Napep (shekara 3) - (Sabon farashi: N5000; Tsohon farashi: N3000)

Lasisin Babur/Keke Napep (shekara 5) - (Sabon farashi: N8000; Tsohon farashi: N5,000)

Kashi 40% na motocin da ake kawowa Najeriya daga waje na sata ne, Ministar Kudi

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta yi wa tsohon Gwamna da wasu mambobin APC 5 tambayoyi kan taron kin jinin Buhari

Ministar kudi da kasafin kudi, Hajiya Zainab Ahmed, a ranar Alhamis ta bayyana cewa akalla kashi 40% na motocin da aka shigo da su Najeriya na sata ne.

Hajiya Shamsuna ta bayyana hakan ne a taron wayar da kai kan sabon tsarin rijistan motoci ta kasa watau National Vehicle Registry (VREG) a Abuja, rahoton Tribune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel