Gwamnati za ta sallama filayen tashi da saukar jirgin Kano, Legas, Ribas da Abuja

Gwamnati za ta sallama filayen tashi da saukar jirgin Kano, Legas, Ribas da Abuja

  • Gwamnatin Tarayya za ta rabu da ikon wasu filayen jirgin sama na kasar nan
  • Ma’aikatar harkokin jirage ta fitar da sanarwa, tana gayyatar duk masu sha’awa
  • Za a ba ‘yan kasuwan damar mallakar wasu bangarori na filayen tashin jirgin

Legas - Gwamnatin tarayya ta fitar da takardar da ke nuna cewa za ta mallaka wa masu bukata manyan filayen tashi da saukar jirgin sama da ke kasar nan.

Gwamnati ta fitar da sanarwa

Punch ta ce Sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin jiragen sama na kasa, Hassan Musa, ya bada wannan sanarwa a wani jawabi da ya fitar a garin Legas.

Wannan sanarwar ta fito ne ta bakin darektan yada labarai na ma’aikatar harkokin jiragen saman, James Odaudu, a jiya, ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, 2021.

Filayen jirgin da gwamnati za ta rabu da su, su ne; babban filin Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja, babban filin Murtala Muhammed da ke garin Legas.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Sake Kashe Mutum 7 a Jos Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai

Sai filin Malam Amınu Kano da ke garin Kano, da babban filin jirgin garin Fatakwal, a jihar Ribas.

Wace riba gwamnati za ta samu daga tsarin?

Hassan Musa yace za a damka filayen jirgin saman ne kamar yadda dokokin kasa da tsarin National Policy on Public-Private Partnership suka yi tanadi.

Nnamdi Azikiwe International Airport
Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na garin Abuja Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Musa yace ana sa rai a gyara filayen tashi da saukar jirgin saman, a kuma nema wa mutane aikin yi, tare da bunkasa kamfanonin cikin gida da wannan yarjejeniya.

“Gwamnatin tarayya ta karkashin ma’aikatar harkokin jiragen sama na tarayya, tana karbar takardu daga masu kula da filayen jirgi/ma’aikata/masu kudi domin neman a damka masu wasu tashoshin filaye jirgin saman a karkashin yarjejeniyar mutum da gwamnati.”
“Damka wani bangare na manyan filayen tashi da saukar jirgin saman yana cikin shirin da gwamnatin tarayya ta yi a ma’aikatar domin cigaban wannan fanni.”

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

NAN ta ce dole duk wanda zai gabatar da takarda ya zama ya san kan aikin jirgin sama. Za a kai sunan kamfani, takardun rajista da kuma rahoton haraji da sauransu.

Hadarin jirgin yaki a Kaduna

A kwanakin baya ne aka samu labari maras dadi na wani jirgin sojojin saman Najeriya da ya fadi a wani yankin jihar Kaduna yayin da yake fatattakar wasu 'yan bindiga.

Rahoto ya bayyana cewa, jirgin ya taso daga jihar Adamawa ne domin ya yaki 'yan bindigan da su ka addabi mutanen Kaduna. A karshe wannan jirgin bai koma gida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng