Ba zamu kara kudin mai zuwa N380 tukun, Ministan mai ya jaddada
- Gwamnatin tarayya ta ce babu ranar kara farashin litan man fetur
- Mai magana da yawun karamin ministan mai ya jaddada hakan
- Gwamnoni a baya sun bukaci a kara farashin zuwa N380 ga lita
Watanni uku bayan gwanonin Najeriya sun bukaci gwamnati tarayya ta kara farashin man fetur zuwa N380, gwamnati ta jaddada cewa har yanzu tana tattaunawa da yan kwadago.
Gwamnati ta jaddada cewa har yanzu bata kammala tattaunawa da yan kwadago ba saboda haka ba za'a kara kudin ba.
Garba Deen Muhammad, mai magana da yawun ministan man fetur, Temipre Sylva, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a.
Garba ya ce zai sake jaddada matsayar maigidansa wanda shine matsayar gwamnatin tarayya.
Garba yace yace mutane da yan kasuwarn mai su cigaba da maganganunsu yadda suka ga dama amma gwamnati ba zata canza kudin mai ba yanzu.
Yace:
"Gaskiyar lamarin shine babbar abinda zai sa mu yanke wani shawara shine idan mun cima matsaya da kwadago. Saboda haka duk abinda gwamnoni ko wani zai fasa, kungiyar kwadago saurara."
"Har yanzu muna tattaunawa da kungiyar kwadago. Ba zamu yanke wani shawara ba har sai an gama tattaunawa. Saboda haka kowa ya fadi abinda ya ga dama."
Yayinda aka tambayesa lokacin da za'a gama tattaunawa da kwadafo, Garba Deen ya ce gwamnatin tarayya bata yanke ba.
A kara farashin litan man fetur zuwa akalla N380, Gwamnonin Najeriya 36 sun yi ittifaki
A kwanakin baya, kungiyar gwamnonin Najeriya NGF karkashin Gwamna Kayode Fayemi, ta kafa kwamiti na musamman domin duba lamarin cire tallafin man fetur.
Za ku tuna cewa shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, ya bayyana a kowani wata ana kashe N120bn don biyan kudin tallafi.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, wanda shine shugaban kwamitin ya gabatar da rahoton bayan tattaunawa da sukayi.
El-Rufa'i yace,
"Ana kashe tsakanin N70bn da N210bn kowani wata don kawai a cigaba da sayar da litan mai a N162, wannan ko uwar kudi bai kai ba kuma kudin dake shigowa gwamnati zai ragu da N50bn a kowani wata."
"Ta wani dalili zamu cigaba da sayar da mai a N162? "
Asali: Legit.ng