Fusatattun Mazauna Kauye sun Sheke Matashin da ya Kashe Abokinsa kan Rikicin Gona

Fusatattun Mazauna Kauye sun Sheke Matashin da ya Kashe Abokinsa kan Rikicin Gona

  • Fusatattun ‘yan kauyen wuraren Sabongida dake garin Iware karkashin karamar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba sun bankawa mutum mai suna Jacob wuta
  • Ana zargin Jacob da kashe abokinsa, Mathies bisa cin amana bayan ya yi hayarsa yayi masa aiki a gona amma ya lamushe kudin kuma yaki yin aikin
  • Sai da matasan kauyen suka yi wa Jacob dukan kawo wuka sannan suka sa masa taya suka banka masa wuta kafin su kona gidansu kurmus

Ardo-Kola, Taraba - Fusatattun ‘yan kauyen wuraren Sabongida dake garin Iware karkashin karamar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba sun kashe wani mutum wanda ya kashe abokinsa sakamakon cin amana.

Daily Trust ta tattaro bayanai akan yadda wanda ‘yan kauyen suka kashe Jacob wanda yaci amanar abokinsa Mathies Michael, wanda yayi hayarsa don yayi masa aiki a gonarsa ta masara dake kauyensu amma ya lamushe kudin yaki yin aikin.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Arewa 31 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari a kotu kyauta

Fusatattun Mazauna Kauye sun Sheke Matashin da ya Kashe Abokinsa kan Rikicin Gona
Fusatattun Mazauna Kauye sun Sheke Matashin da ya Kashe Abokinsa kan Rikicin Gona. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Marigayi Mathies ya fusata bayan ya je gonar ya gano cewa bai yi aikin ba. Ya isa wurin abokinsa cikin fushi yana tuhumarsa shine ya danna masa wuka ya kashe shi.

Yaya lamarin ya faru?

Ganau sun ga yadda Jacob yayi wa Mathies yankan rago.

Bayan faruwar lamarin, Mathies ya iso gidana yana ihu yana cewa abokina Yakubu ne ya yankani’, ‘Abokina Yakubu ne ya yankani, a cewar ganau din da ya bayar da shaidar.

Ya kara da sanar da yadda ‘yan uwan mamacin suka sanar da al’umma su fara neman wanda ya kashe shi, Daily Trust ta ruwaito.

Sai da suka yi wa Jacob dukan kawo wuka sannan suka banka masa wuta ya kurmushe.

Me mahaifin mamacin yace?

Mahaifin mamacin, Micheal Adamu, ya sanar da Daily Trust cewa da misalin karfe 6:15am yaji dansa yana ihu yana cewa abokinsa Yakubu ya sharba mishi wuka.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Yaro mai shekara 9 yayi garkuwa da dan makwabta mai shekara 4 a Kano

Ni sifeta ne a NSCDC amma ina ta ciwo na tsawon shekaru 2.
Da misalin karfe 6:15 na safiya naji ihun dana yana fada mana cewa abokin shi ya yanke shi a wuya a taimaka a kai shi asibiti amma kafin a kai ga tafiya dashi ya fadi ya mutu, a cewar Micheal.
Shugaban yankinsu ne ya sanar da ‘yan sanda kuma kafin su iso mun shigar da gawarshi cikin dakina.
Lokacin da ‘yan sandan suka zo sun so daukar gawar amma na rokesu su bar shi mu birne shi cikin mutunci,” a cewarsa.

Shugaban kauyen, Hyginus Jonah wanda ya kai Daily Trust har rusasshen gidan wanda ake zargin ya yi kisa ya ce ‘yan sanda sun kasa dakatar da komai.

Bayan Daily Trust ta kai ziyara gidan wanda ake zargin ya gano yadda aka rushe dakuna 3 kuma aka banka musu wuta.

Bayan an nemi jin ta bakin kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Taraba, ASP Abdullahi Usman, ya ce bashi da wani rahoto akan lamarin amma zai sanar idan ya bincika.

Kara karanta wannan

Wata Amarya Ta Hallaka Angonta Kwanaki Kadan Bayan Sun Yi Auren Soyayya

Asali: Legit.ng

Online view pixel